Zan gyara wa ’yan sanda zama —Buhari
Buhari ya umarci shugaban ’yan sanda a hukunta jami’ansa masu cin zalin ’yan kasa
Shuguga Buhari a gana da Shugaban ‘Yan Sandan
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba wa ’yan Najeriya tabbacin kawo karshen zaluncin ’yan sanda a kasar.
Buhari bayan ganawarsa da Shugaban ’Yan Sanda a daren Asabar kan halin da rundundar ke ciki ya ba da tabbacin cewa zai gyara wa jami’an rundunar zama.
“Ina samun bayanai akai-akai kan kokarin kokarin magance cin zali dan karya doka da ’yan sanda ke yi.
“Hakan zai tabbatar da ganin ana hukunta su don su daina karya dokoki”, inji shi.
- ’Yan kwaya sun kashe jami’in NDLEA
- An rufe hanya saboda zaben Gwamnan Ondo
- Hotuna: Yadda wasu Makafi ke sana’ar nika
Ya ci gaba da cewa, “Na umarci shugaban ’yan sanda ya biya wa ’yan Najeriya bukata game da ketare iyakan ya kuma tabbatar da an hukunta jami’an da aka samu da laifi.
“Ina ba da hakuri yayin da ’yan Najeriya ke ci gaba bayyana ra’ayoyinsu cikin lumana”.
Gabanin haka Hadimin Shugaban Kasa na Shafukan Zumunta, Bashir Ahmad, ya ce shugaban ya samu rahoton irin cin zalin da jami’an rundunar na FSARS ke yi.
Bashir ya ce ya bayyana yakinin cewa Shugaban zai dauki kwakkwaran mataki bayan tattaunawasa da Shugaban ‘yan sandan.