Fubara ya janye neman takarar Gwamna a APC
Shi shugabanci abu ne da ke buƙatar sadaukarwa. Akwai lokacin da dole a haƙura da buƙatar kai domin maslahar mutane.
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya janye daga neman tikitin takarar kujerarsa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, mai taken “Ƙudirina na janyewa daga zaɓen fidda gwanin APC”, in da ya yi alƙawarin mara wa duk wanda ya samu nasara goyon baya.
- Sabon Masallacin Fadar Zazzau ya sake ruftowa ana tsaka da aiki
- PDP ta tabbatar da Dankwambo a matsayin ɗan takarar Sanatan Gombe Ta Arewa
“Bayan dogon nazari da na yi da shawarwari da dangi da abokai, da abokan aiki, na janye daga zaɓen neman cikin gida na kujerar Gwamna a APC. Kuma na yi hakan ne domin mara wa duk wanda ya samu nasara goyon baya.”
“Shi shugabanci abu ne da ke buƙatar sadaukarwa. Akwai lokacin da dole a haƙura da buƙatar kai domin maslahar mutane.
“A wannan lokacin, zaman lafiya da haɗin kan mutane ne a kan gaba fiye da komai
“Ga masu goyon bayana da suka tsaya tsayin daka tare da ni tun daga farko, suka bani goyon baya da ƙarfinsu da dukiyarsu da addu’o’i, ina matuƙar godiya a gare ku.
“Na san ba za ku ji daɗin abin da na yi ba, amma ina so ku sani abin da kuka yi ba zai faɗi a banza ba.”
Fubara, ya kuma ce tsananin son da yake yi wa jiharsa ta Ribas ce ta sanya ya ɗau wannan matakin, tare da miƙa godiya ga Shugaba Bola Tinubu saboda goyon baya da ƙwarin gwiwar da yake bashi.