Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas

Na yi iya ƙoƙari don tabbatar da an kare dimokuraɗiyya da ci gaban mutanen jihar amma majalisar ta riƙa hana ruwa gudu.

Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya buƙaci al’ummar jihar da su zauna lafiya sannan su kasance masu kiyaye doka da oda.

Fubara ya yi kiran ne safiyar wannan Larabar bayan da yammacin Talatar jiya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi da mataimakiyarsa da duk ’yan majalisar dokoki sannan ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar.

Cikin sanarwar da ya fitar, Mista Fubara ya jaddada cewa abubuwan da ya yi, ya yi su ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki don kare martabar al’ummar jihar.

‘Mun yi ƙoƙarin yin sulhu’

Fubara ya bayyana cewa tun bayan hawansa gwamnati, ya kasance yana aiki ne don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce duk da tankiyar siyasa, ya ci gaba da gudanar da aiki don tabbatar da tsaro da inganta rayuwar mutanen Jihar Ribas.

Ya ƙara da cewa bayan shugaban ƙasa ya shiga tsakani domin kawo zaman lafiya, ya kiyaye duk yarjejeniyar da aka cimma, ciki har da karɓar kwamishinonin da suka yi murabus a baya.

Bayan haka, gwamnan ya ce ya amince da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke domin mayar da jihar kan turbar da doka da oda suka tanadar.

‘Majalisar dokokin Ribas ta hana ruwa gudu’

Gwamnan ya ce duk da ƙoƙarin da gwamnatinsa ta yi domin samar da zaman lafiya, ’yan majalisar dokokin jihar sun kawo cikas.

Ya ce yana aiki ne don tabbatar da an kare dimokuraɗiyya da ci gaban mutanen jihar amma majalisar ta riƙa hana ruwa gudu.

A cewarsa, duk da saɓanin siyasa da ake fama da shi, gwamnatinsa na biyan albashin ma’aikata tare da aiwatar da manyan ayyuka don ci gaban jihar.

Fubara ya bayyana cewa duk da ƙalubalen siyasar, ya tabbatar da jihar na cikin kwanciyar hankali kuma babu wata barazanar tsaro da ake fuskanta.

A ƙarshe Fubara ya buƙaci mutanen jihar da su zauna lafiya tare da guje wa duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tuntuɓar hukumomin da suka dace don kare dimokuraɗiyya da tabbatar da ci gaban jihar.

Gobara ta kashe yara 3, ta jikkata 13 a Yobe

Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas

Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira

Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas