Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas
Gwamnan ya sauka amma babu labarin ko gidan gwamnatin jihar ya nufa.
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya dawo bayan shafe tsawon lokaci baya jihar biyo bayan sanya dokar ta-ɓaci da Shugaba Tinubu ya yi.
A ranar Laraba ne Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci, wadda tsohon Hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Ibok-Ekwe Ibas (rtd), ya jagoranta.
- ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe
- An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki
Magoya bayan gwamnan sun taru a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal domin tarbarsa bayan dakatar da shi na tsawon watanni shida, amma daga baya suka watse bayan shafe lokaci suna jira ba tare da ganinsa ba.
Da safiyar ranar Juma’a, magoya bayan suka koma Filin Jirgin Sama na Fatakwal.
Jirgin da ya ɗauko gwamnan ya sauka a filin da misalin ƙarfe 12 na rana.
Ya gaisa da magoya bayansa a filin jirgin kafin daga bisani ya shiga mota tare da ayarinsa suka tafi.
Babu tabbacin cewar ko gidan gwamnati ya nufa kai-tsaye domin ci gaba da gudanar da harkokin mulki.