Fulani a Kwara sun kafa kungiyar sintiri
Shugabannin al’ummar Fulani mazauna Jihar Kwara da kungiyar Miyatti Allah sun yi taron zaman lafiya a fadar Sarkin Fulanin jihar da ke Ilorin.Yayin taron, wanda ya samu halartar sarakunan Fulani na daukacin kananan hukumomin jihar, sarikin Fulanin jihar ta Kwara, Hardo Mu’azu Buruku ya shaida wa Aminiya cewa ya tara shuwagabannin ne domin su yi […]
Shugabannin al’ummar Fulani mazauna Jihar Kwara da kungiyar Miyatti Allah sun yi taron zaman lafiya a fadar Sarkin Fulanin jihar da ke Ilorin.
Yayin taron, wanda ya samu halartar sarakunan Fulani na daukacin kananan hukumomin jihar, sarikin Fulanin jihar ta Kwara, Hardo Mu’azu Buruku ya shaida wa Aminiya cewa ya tara shuwagabannin ne domin su yi taron zaman lafiya, la’akari da zaman tsoro da Allah Ya jarrabe su da shi, inda yara matasa suke daukar dattawa su kai su daji har sai an ba su kudin fansa.
“Ana ba su makudan kudaden da suke bukata, su je su barnata su a banza kuma mun lalubo, mun gano cewa mafi yawansu ’ya’yanmu ne da suka kangare. Duk da dai ba su kadai ba ne amma su suka fi yawa. Don haka muka shirya taron, na kuma ba su umarni su je su tsamo samarin da suka yadda da su, su kafa kungiyar ’yan sintiri. Su je ga Sarkin Ilorin da Gwamnan Jihar Kwara su sanya masu hannu, su kuma tuntubi jami’an tsaro domin a lalubo bakin zaren.” Inji Hardon.
A nasa bangaren, sarkin Fulanin Bogesagu a Jihar Kwara, Alhaji Abubakar Harange ya shaida wa Aminiya cewa neman hadin kai da zaman lafiya ne musabbabin taron kuma a yanzu haka kwalliya ta soma biyan kudin sabulu; domin sun fara ganin haske a lamarin.
Shi ma sarki Fulani Alhaji Adamu Manuga Kwara, ya shaida cewa halin matsin da suka samu kansu ne ya sanya ya zama wajibi su dinga shirya iren-iren wannan taron, domin kadan daga cikin matsalolinsu su ne rashin dajin kiwo da yawan sace-sacen da ake danganta su da Fulani.
A binciken da Aminiya ta yi, ya nuna cewa a da an san ’ya’yan Fulani da kunya da kara da kyawawan dabi’u, sai dai a yanzu ana samun baragurbi a cikinsu, a sakamakon sauyin lamari na rashin dajin kiwo da matsalar nan ta barayin shanu, wanda yake tilasta wasu bata-garin matasan su shiga harkokin assha. Domin daman su ba karatu suka yi ba, ba ilimin boko ba na addini, kiwo kawai suka sani. To, da zarar sun gaza samun damar yin kiwo sai su rungumi mugunyar hanya. Wannan shi ne dalilan da ya sa shuwagabannin Fulanin ke yin kiraye-kiraye na muhimmancin sanya ’ya’yan Fulani a makarantu, domin su fadada hanyoyin dogaro da kai.