Fulani ba ’yan ta’adda ba ne – Sarkin Musulmi
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana damuwarsa kan karan-tsana da kalmomi maras dadi da ake kiran al’ummar Fulani da su, inda ya ce ya zama dole su fito su kare jama’ar Fulani da kungiyar Miyetti Allah domin su ne iyayen kungiyar. Sarkin Musulmin ya yi wadannan kalamai ne a ranar Talatar da […]

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana damuwarsa kan karan-tsana da kalmomi maras dadi da ake kiran al’ummar Fulani da su, inda ya ce ya zama dole su fito su kare jama’ar Fulani da kungiyar Miyetti Allah domin su ne iyayen kungiyar.
Sarkin Musulmin ya yi wadannan kalamai ne a ranar Talatar da ta gabata a fadarsa yayin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta kasa, inda ya ce “Da ka ji an kashe mutum daya a wani wuri sai a lika wa Fulani, duk wani abu marar kyau Fulani ne abin da sam ba haka ba ne.”
Ya kara da cewa, “Wannan ba shi ke nuna Fulani ba su aikata laifi ba, don kowace kabila tana da batagari a cikinta, a cikin kashi 100 na mutane, fiye da kashi 70 dinsu mutanen kwarai ne kuma ka ce su batagari ne a yi wa Fulani adalci.”
Sarkin Musulmin ya kara da cewa, “Mutumin da ba ruwansa da kayan gwamnati kiwon shanunsa ne kawai damuwarsa amma da zarar an kashe mutane sai a ce Fulani ne ke aiwatarwa, Bafillace mai shanu 500 ko 1000 to ina ya bar shanun ya je ya kashe mutane? Mu shugabanni ne na addini za mu yi adalci ga kowa domin babu zaman lafiya matukar aka rasa gaskiya da tsoron Allah da adalci. Mutumin da ya dawo cikin daji da zama tare da ’ya’yansa da matansa kuma dokar kasa ta yarda mutum ya zauna inda yake so ba tare da wata tsangwama ba.”
Ya ce a kashe Fulani 800 ko dubu ba a magana amma in aka kashe mutum goma a yayata cewa Fulani ne to su wadanda aka kashe ba mutane ba ne? “Ba mu ce a fifita mu ba, amma a yi mana adalci, ba mu fi kowa ba a tashi tsaye da sunan Allah tun daga kan Shugaban kasa har gwamnoni su ji tsoron Allah. Fulani ba ’yan ta’adda ba ne ba su yawo da bindiga kalmar da ake amfani da ita ko’ina ba mu yarda da ita ba, jami’an tsaro ku yi aikinku duk mai yin ta’addanci a kama shi. Mu ne shugabannin Fulani ba mu kunyar mu fadi mu Fulani ne mu ba ’yan ta’adda ba ne shugabanni ne da ke tsoron Allah da son zama lafiya da ci gaban kasa,” inji shi.
Da ya juya kan sababbin shugabannin na Miyetti Allah, Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce, “Ina son in jawo hankalinku akwai aiki a gabanku ana abubuwa da yawa na ta’addanci a kasar nan a ce Fulani ne, dole ku tashi tsaye ku binciko mana su wane ne ke amfani da sunanku suke shiga kauyuka da garuruwa ku zauna da shugabanni daban-daban, ku hada rahoto ku kawo mana shi cikin wata biyu. A rahoton ku fada mana abin da ya kamata mu yi mu shugabanni kuma za mu yi insha Allah, aiki yana gabanku ku sadukar da kai ku gaya mana su wane ne ke yin wannan kisan a kasa? Fulani ne ko wadansu ke yi a dora wa Fulani ana samun rigima ta Fulani da makiyaya?”
Ya ja hankalin jama’a musamman ’ya’yan kungiyar Miyetti Allah da ya ce tun kafuwarta su ne jagororinta, su sani cewa ba hannunsu a Kotel Hore, ba su tuntubar su a ayukkansu Miyetti Allah (MACBAN) ce tasu.
Sabon Shugaban kungiyar Miyati Allah ta kasa (MACBAN) da aka rantsar a karo na biyu Alhaji Muhammad Kiruwa Ardon Zuru ya gode wa Sarkin Musulmi da dukan sarakunan Daular Usmaniyya kan goyon bayan da suke ba su kuma ya yi alkawari daga gobe (shekaranjiya Laraba) za su fara aikin da aka dora musu kuma za su kawo rahoto kasa da wata biyun da aka ba su, inda ya yi fatar aikin ya zama silar warware matsalar makiyaya da manoma da rikicin kabilanci a kasar nan.
“Aikin da aka ba ni a tura ni gaba ne kadan don mun yi jadawalin inda za mu fara, gwamnonin Arewa musamman su ba mu damar yin aikin ba kamar inda aka fito ba ciwon an gano maganinsa. Kan dokar hana kiwo a fili wadansu gwamnoni sun ja da baya domin dokarsu ta kalubalanci ta kasa kuma dokar kasa ce gaba,” inji Kiruwa.
Da ya juya kan ‘yan Kotal Hore da Sarkin Musulmi ya nesanta kansu da su, ya ce “Ba mu kore su daga cikinmu ba, kawai sun balle ne ko don rashin cin zabe ko neman wata dama, in mutum bai samu ba sai ya yi hakuri da ’yan uwansa cikin kungiyar da ta yi shekara 40 ba ya kirkiri wata kungiya ba, ba kin gidan uwa da uba ba. Domin duk gidan da ka shiga ba ka jin dadinsa kamar naku don haka su dawo gida tunda ba korarsu aka yi ba.”