Fulani makiyaya a Oyo sun nemi a zauna lafiya da manoma
Shugaban kungiyar Fulani ta Jamu-Nati-Fulbe na kasa baki daya, Alhaji Salihu kadir ya yi gargadi manoma a yankin Igangan na Jihar Oyo cewa su daina zuba guba a cikin abincin dabbobinsu da suke ci suna mutuwa. Inda ya ce tura ta kai su bango, sun gaji da irin barnar da ake yi masu a wannan […]

Shugaban kungiyar Fulani ta Jamu-Nati-Fulbe na kasa baki daya, Alhaji Salihu kadir ya yi gargadi manoma a yankin Igangan na Jihar Oyo cewa su daina zuba guba a cikin abincin dabbobinsu da suke ci suna mutuwa. Inda ya ce tura ta kai su bango, sun gaji da irin barnar da ake yi masu a wannan yanki.
A wani jawabin da ya yi na gargadi a wajen taron gaugawa da kungiyar tasu ta kira, tare da da hadin gwiwar shugabannin Fulani na Jihar Oyo a garin Igangan a Litinin da ta gabata, shugaban ya ce: “Yau makonni biyu da suka gabata ke nan da manoma suka kashe mana shanu guda 15, bayan da suka ci guba a kan burtali. Bayan sun kashe mana dabbobi, manoman sun sun auka wa yaranmu da sara da suka da makami tare da lakada masu duka. Yanzu haka yaranmu su 10 suna kwance a asibiti da suke jinyar raunuka da suka samu a dalili wannan al’amari.”
Ya ce yaransu sun yunkura domin mayar da martani amma suka dakatar da su daga yanke wa kansu hukunci. “Wannan ne dalilin kiran wannan taro na gaugawa da muke sanar da mahukunta irin matakin da za mu dauka na mayar da martani ga manoman idan suka ci gaba da yi mana barna ba tare da mahukunta sun yi maganin matsalar ba,” inji shi.
Shugaban ya nuna wa mahalarta taron irin busassun doya da rogo da masara da ake barbada masu guba kuma aka ajiye a kan burtalin shanun da suke ci suka mutu.
“Me ya sa ake ajiye irin wannan guba a kan hanyoyin kiwon shanu ba cikin gonaki ba? Suna so su kore mu daga wannan wuri ne amma ba za su yi nasara ba, domin mu ma ’yan Najeriya ne. Kuma akwai da yawa daga cikinmu masu shekara 60 zuwa fiye da 70 da aka haife mu a nan garin Igangan, ba mu san ko’ina ba sai Igangan. Idan ma sun kore mu, ina za mu je”
Tsohon shugaban riko na karamar Hukumar Ibarapa ta Arewa Stephen Adegboyege, wanda ya halarci taron ya tunatar da manoman yankin Igangan game da zaman lafiya a tsakaninsu da makiyaya.
“Akwai miliyoyin kabilun Yarabawa da suke zaune a Arewacin Najeriya amma ba mu taba jin ana yunkurin korarsu daga can ba. A wannan sashe ne mutanenmu suke yin irin wannan yunkuri na korar baki, wanda haka ne yake haifar da tashin hankali a tsakanin al’ummomin kasar nan,” inji shi.
Shi kuwa Baale Agbe wato shugaban manoman kauyen Tapa, Cif Oludele Ayedepo alkawari ya yi cewa zai tabbatar da isar da sakamakon taron da matakin da Fulanin suka dauka ga mutanensa.
Wasu daga cikin Shugabannin Fulanni da suka halarci taron na Igangan sun fadi ra’ayinsu kan yadda suke ganin za a iya yin maganin wannan matsala. Sun ce “akwai yarjejeniyar biyan kudin diyyar gonakin da dabbobinmu suka lalata da biyan dabbobin da aka kashe mana.
A bangarenmu muna girmama yarjejeniyar wajen biyan irin wannan kudi da manoma suke hada baki da ’yan sanda suna tatsar dimbin kudade daga hannunmu. Amma ba a taba biyan mu diyyar shanun da aka kashe mana ba. Sai idan kowane bangare ya girmama wannan yarjejeniya ne za a samu zaman lafiya.”
Taron ya jinjina wa Sarkin garin Eruwa a kan irin matakin adalci da yake dauka a kowane lokaci aka kai masa batun rikici tsakanin manoma da makiyaya. An gudanar da taron ne a gaban wakilan rundunonin tsaro na ’yan sanda da soja da SSS da NSCDC.