Fulani makiyaya na neman a yi maslaha da manoma – Ardo Manga
Sarkin Fulani Oru Efeledo Ilorrin, Jihar Kwara, Alhaji Ardo Adamu Manuga ya koka akan irin abin da ya ce matsalolin da Fulani makiyaya ke fuskanta a kasar nan, inda aka mayar da Fulanin tamkar saniyar ware, ko wadan da ba ‘yan kasa ba.Alhaji Ardo Adamu Manuga, ya yi wannan furucin ne a zantawarsa da wakilinmu […]
Sarkin Fulani Oru Efeledo Ilorrin, Jihar Kwara, Alhaji Ardo Adamu Manuga ya koka akan irin abin da ya ce matsalolin da Fulani makiyaya ke fuskanta a kasar nan, inda aka mayar da Fulanin tamkar saniyar ware, ko wadan da ba ‘yan kasa ba.
Alhaji Ardo Adamu Manuga, ya yi wannan furucin ne a zantawarsa da wakilinmu a garin Benin, a wata ziyararsa ta sadar da zumunci ga ’yan uwansa Fulani makiyaya, mazauna Jihar, inda ya ce na farko al’ummarmu suna bukatar gwamnati ta ba su ’yanci na tafiyar da rayuwarsu da dabbobin acikin kasar nan, ba tare da nuna banbanci ba.
“Muna son gwamnati ta shiga tsakaninmu da manoma, ta tsaga mana burtali da wuraren kiwon dabbobinmu, da mashayarsu. Idan gwamnati ta yi mana wannan, to, lallai na tabbatar za a samu maslahar zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya. Domin Fulani makiyaya a kodayaushe suna biyayya ga tsarin mulkin kasa. Don haka su ba su daukar doka a hannu, kamar yadda nake ganin yake faruwa wasu suke yi idan wani abu kadan ya hada su da Fulanin,” a cewarsa
Sarkin Fulanin, ya kalubanci mahukuntan kasar nan da cewa suna daukar matakan tsanantawa akan makiyaya da rashin kulawa da hakkin da ya ya shafi bangaren makiyayan.
‘’Mahukunta a kasar nan sun maida makiyaya tamkar saniyar ware ba su damu da hakkinmu na ‘yan kasa ba,” inji shi.’’
Kan batun ilimin ‘’ya’yan makiyaya, ya ce wasu masu hana ruwa gudu ne a cikin ma’aikatan gwamnati da wasu ‘yan siyasa suke neman bata sunan Fulanin, da cewa wai ba su damu da ’ya’yansu su sami ilimin addini ma, balantana na zamani.
Da ya juya kan barnar gonakin jama’a, Sarkin ya ce Fulani makiyaya masu bin doka da oda ne, don haka idan har aka samu kuskure da ya shafi barnar gona muna biyan masu gonan abin da muka shirya da su gwargwadon hali.
Dangane da zargin da ake yi wa matasansu, na cewa wasu daga cikinsu suna aikata ta’addanci ga ’yan uwansu Fulani ta hanyar abka musu da fada, da kwace dukiya, sai ya ce ‘ai batun irin wannan ba zan iya bayar da shaida akan hakan ba, kuma ba na cewa ko karya ba, domin abin ya zama ruwan dare gama duniya sai dai addu’a.