Fulani Makiyaya sun fi kowa ganin tasku – dungiyar Miyetti-Allah

Shugaban dungiyar Fulani Makiyaya Miyetti reshen shiyyar Arewa-maso-Gabas Alhaji Mai Aliyu Usman ya dalubalanci shugabannin dasar nan dangane da yadda suke jan dafa kan abin da ya shafi rayuwar makiyaya a dasar nan.Shugaban ya bayyana hakan ne a garin Damaturu, ya ce “ana cin zarafin makiyaya da yi musu kisan gilla tare da sace dabbobinsu […]

Fulani Makiyaya sun fi kowa ganin tasku – dungiyar Miyetti-Allah
Fulani Makiyaya sun fi kowa ganin tasku – dungiyar Miyetti-Allah

Shugaban dungiyar Fulani Makiyaya Miyetti reshen shiyyar Arewa-maso-Gabas Alhaji Mai Aliyu Usman ya dalubalanci shugabannin dasar nan dangane da yadda suke jan dafa kan abin da ya shafi rayuwar makiyaya a dasar nan.
Shugaban ya bayyana hakan ne a garin Damaturu, ya ce “ana cin zarafin makiyaya da yi musu kisan gilla tare da sace dabbobinsu a sassa da dama na dasar nan wannan yana ci mana tuwo a dwarya. Kuma hakan yana nuna irin rashin gatan da suke fuskanta a cikin al’umma duk da dimbin gudummawar suke bayarwa.”
Ya dara da cewa makiyaya da ke yankin jihohin arewa maso gabas “sun fi kowa ganin tasku domin rikicin da yankin ke fama da shi na ya yi sanadiyyar halaka mambobin dungiyar da dabbobinsu da dama wanda a ma fi yawan lokaci mambobin dungiyar kan fada halin gaba kura baya siyaki.”
Daga nan ya ce “muna rodon shugaban dasa da ma duk wanda alhakin kula da al’umma ke wuyansu da su gaggauta kawo dauki ga makiyayan yankin Arewa-maso-Gabas ganin cewa suna cikin halin hawula’i domin da yawansu an raba su da dukiyarsu, don haka idan manomi ko dan kasuwa ya rasa dukiyarsa sanadiyyar afkawar wani iftila’i gwamnati kan kai musu dauki don haka shi ma makiyayi akwai budatar a yi masa haka.”
A darshe ya tabbatar wa da mambobin dungiyar da ke jihohi shida na Arewa-maso-Gabas cewa za a gudanar da zabe mai adalci nan gaba kadan.