Fulani masu kaunar zaman lafiya ne – Shugaban Miyetti Allah

Sabon Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders reshen Jihar Nasarawa, Alhaji Husseini Muhammed ya ce Fulani makiyaya da ke tafiya wasu kauyukan Jihar Binuwai daga Jihar Nasarawa suna tafiya ne don neman wa shanunsu abinci ba don tashin hankali da al’ummomin jihar ba, sabanin yadda wasu a jihar ke zarginsu.Ya ce kasancewa Allah Ya albarkaci […]

Fulani masu kaunar zaman lafiya ne – Shugaban Miyetti Allah
Fulani masu kaunar zaman lafiya ne – Shugaban Miyetti Allah

Sabon Shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders reshen Jihar Nasarawa, Alhaji Husseini Muhammed ya ce Fulani makiyaya da ke tafiya wasu kauyukan Jihar Binuwai daga Jihar Nasarawa suna tafiya ne don neman wa shanunsu abinci ba don tashin hankali da al’ummomin jihar ba, sabanin yadda wasu a jihar ke zarginsu.
Ya ce kasancewa Allah Ya albarkaci Jihar Binuwai da abinci da ruwa da shanu ke bukata sosai shi ya sa wadannan Fulani ke tafiya wadannan kauyuka don kiwon shanunsu ba don ta da fitina ba.
Daga nan ya karyata zargin da wasu ke yadawa a Jihar Binuwai bayan wani mummunan hari da wasu ’yan bindiga suka kai wa wasu kauyuka a jihar da ya yi sanadiyyar rasa rayukan akalla mutum 300, inda ake zargi cewa wasu Fulani ne da ke shigo jihar daga Jihar Nasarawa inda suke kai hare-hare suna kashe mutane a kauyuka ba gara ba dalili.
A cewarsa dokar kasar nan ta bai wa kowa damar tafiya ko ina a fadin kasar nan. Saboda haka a cewarsa bai kamata ace wasu a jihar suna irin wannan zargi ba, tun da ba a kama wani mutumin Fulani da ke da alaka ga lamarin ba a halin yanzu maimakon haka a cewarsa a bar jami’an tsaro su ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.
Da yake bayyani game da shirye-shiryensa a matsayin sabon shugaban kungiyar a jihar Alhaji Huseini Muhammed ya ce zai kafa kwamitoti daban-daban da suka hada da na ilimi da tabbatar da tsaro da fyade da shawo kan satar shanu da sauransu. Ya ce wadannan kwamitoti za su rika tabbatar al’ummar Fulani a jihar baki daya musamman wadanda ke karkara sun samu ilimin addini da na zamani don canja rayuwansu. Hakazalika, za su rika hada kai da jami’an tsaro wajen dakile ayyukan bata-gari tsakani al’ummar Fulani da sauran al’ummar jihar baki daya.
Daga nan sai ya yi amfani da damar, inda ya shawarci gwamnatin tarayya da na jihohi da su bullo da tsare-tsare da za su hana manoma da makiyaya shiga hakin jama’a ta hanyan kayyade yawan shanu da hana Bafullatani kiwon fiye da shanu dubu daya shi kadai da sauransu don kawo karshen rigirgimu tsakanin Fulani makiyaya da manoma a jihar da ma kasa baki daya.
Har ila yau, ya bukace su da su tabbatar suna bai wa shanu rigakafin cututtuka don samar wa al’umma baki daya nama da madara masu inganci don kiyaye lafiyansu.
A makon jiya ne wasu ’yan bindiga suka kai hari a wasu kauyukan Jihar Binuwai, inda suka kashe fiye da mutum 300. Wasu al’ummar jihar na zargin cewa wasu Fulani makiyaya ne suka aikata danyen aikin kuma daga Jihar Nasarawa suke shigowa.