Fulani na cikin tsaka mai wuya

A halin yanzu dai Fulani mazauna kurmi na cikin tsaka mai wuya bisa miyagun ayyukan da ake yawan alakanta su da shi, wanda ya sanya ake barazanar korarsu daga yankin.A ranar litinin din da ta gabata  jami’an ‘yan sanda suka kai wa shugabbanin fulani makiyaya samame a wadansu jihohin kudu maso yamma,  inda suka kame […]

Fulani na cikin tsaka mai wuya
Fulani na cikin tsaka mai wuya

A halin yanzu dai Fulani mazauna kurmi na cikin tsaka mai wuya bisa miyagun ayyukan da ake yawan alakanta su da shi, wanda ya sanya ake barazanar korarsu daga yankin.
A ranar litinin din da ta gabata  jami’an ‘yan sanda suka kai wa shugabbanin fulani makiyaya samame a wadansu jihohin kudu maso yamma,  inda suka kame wadansu daga cikinsu,  abin da ake alakantawa da garkuwar da aka yi da Sanata Iyabo Anisulowo a jihar Ogun,  kwanaki uku da yin garkuwar ne jami’an ‘yan sanda suka yi awon gaba da shugaban kungiyar  Miyyatti Allah reshen juhar Ogun da Alhaji Abdulmuminu da sakataren kungiyar Alhaji Isa Yaro, wadanda har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto suna hannun jami’an ‘yan sanda. Bayanai sun nuna cewa baya ga jihar Ogun, irin hakan ta faru a wadansu jihohin na kurmi.
Jami’an tsaron sun kame shugabbanin fulanin ne bisa hujjar cewa su suka fi kowa sanin bara-gurbin da ke cikinsu da suke addabar jama’a da yin garkuwa da mutane.
A daya bangaren su ma fulanin suna kokawa bisa halin da suka samu kansu a ciki na rashin kwanciyar hankali, saboda addabarsu da satar masu mutane ana karbar kudin fansa. A karshen makon jiya ne kungiyar fulani ta Jumnatil Fulbe ta shirya taro a garin lseyi na jihar Oyo,  Sarkin fulanin Okaka a jihar ya shaida wa Aminiya cewa a wannan yanki na mararrabar jihohin Kwara da Oyo ba a yin mako biyu ba tare da an yi garkuwa da dattijon bafilatani ba, “ a saboda wannan matsala ce ta sanya da yawa daga cikin dattawanmu suke yin kaura suna barin dabobbinsu da iyalinsu domin tsira da ransu,” inji shi.
Shi kuwa shugaban kungiyar cigaban mutanen Arewa, Alhaji Adi Shu’aibu dansudu,  cewaya yi  kafafen yada labarai ba sa yi wa fulani adalci,  domin a cewarsa, sau tari ake cutar da fulanin amma su ba su da bakin fada,  “ matsalar da ta addabi fulani na sace-sacen dattawansu da dabobbinsu babu wanda ya san ana yi,  kamata ya yi ‘yan jarida su rika tsananta bincike,  abu ne nai kamar wuya bafillatani a daji ya bar dukiyarsa ya je yana aikata masha’a,” inji shi.