Fulani na yunkurin halaka kansu kan dokar kiwo – Bodejo

Kungiyar Miyetti-Allah Kautal Hore ta yi hannunka mai sanda ga Gwamnatin Najeriya game da wani shiri da wasu Fulani ke yi na yunkurin hallaka kansu tare da shanunsu, biyo bayan dokar takaita kiwo da gwamnatocin wasu jihohi suka kaddamar.  Shugaban kungiyar ta kasa, Alhaji Bello Bodejo ne ya bayyana haka, a yayin wata zantawa da […]

Fulani na yunkurin halaka kansu kan dokar kiwo – Bodejo

Kungiyar Miyetti-Allah Kautal Hore ta yi hannunka mai sanda ga Gwamnatin Najeriya game da wani shiri da wasu Fulani ke yi na yunkurin hallaka kansu tare da shanunsu, biyo bayan dokar takaita kiwo da gwamnatocin wasu jihohi suka kaddamar. 

Shugaban kungiyar ta kasa, Alhaji Bello Bodejo ne ya bayyana haka, a yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai a ofishinsa da ke Abuja a ranar Talatar da ta gabata. Inda ya bukaci gwamnatin Tarayya da kuma Majalisar Dokoki su shiga batun, don hana fulanin halaka kansu tare da dukiyoyin nasu wajen sake duba wannan doka yadda ya kamata.

Tuni da jihohin Ekiti da Benuwai suka kaddamar da wannan doka ta takaita kiwon shanu a jihohin nasu, bisa dalilan da suka bayar na yawan samun taho-mu-gama da rikice-rikice tsakanin makiyaya da manoma tsawon lokaci.

Haka kuma Bodejo, ya kara da cewa “Hakika wannan doka ta takaita kiwo da aka kakabawa Fulani tamkar yanke hukuncin kisa ne gares su da kuma dabbobin nasu baki daya. Domin babu inda wani bafulatani zai iya rayuwa tare da irin wannan kunci na tkaita masa inda zai zauna ba tare da la’akari da abinda yake bukata shi da dabbobin nasa a kullum ba.”

Sannan shugaban fulanin ya ce, baya ga wannan yunkuri da wasu fulanin key i na halaka kansa tare da shanunsu, wasu kuma da dama sun bace sun yi tafiyarsu ba tare da sanin inda suka dos aba saboda tsaron da suke ji na saba wannan dokar idan an kama su.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, wani bafullatani makiyayi mai suna Mohammed Abdulkadire, ɗan shekaru 56, ya halaka kansa ta hanyar tsunduma cikin kogi a yankin ƙaramar Hukumar Logo ta Jihar Binuwai a ranar Lahadin da ya gabata.

Shugaban kungiyar Miyetti-Allah Cattle Breeders na Jihar Benuwai, Alhaji Garus Gololo ne ya tabbatar wa manema labarai wannan lamari, inda ya ce mamacin ya rasa ransa ne sakamakon mutuwar shanunsa har 200 saboda yunwa da kuma ƙishin ruwa a yankin, wanda yake magidanci ne mai ‘ya’ya 22.

Shugaban na makiyaya ya ƙara da cewa, “Mutumin ya kashe kansa ne saboda, ba wurin da shanunsa za su yi kiwo. Yana mai shirin komawa ƙaramar hukumar Awe ce ta Jihar Nassarawa a lokacin. Amma labarin da ya iso mana shi ne a daidai wannan lokacin an killace ƙaramar Hukumar ta Awe daga shigan makiyayan, an hana duk wani makiyayi shiga cikinta. Don haka muna yin kira ga gwamnatin Tarayya da ta hanzarta sa baki wajen umurtar gwamnatin ta Binuwai da ta janye wannan dokar da ta kafa, kafin Fulanin su rasa dukkanin abinda suka mallaka,” a cewarsa.