Fulani sun kaurace wa kasuwanin Jihar Jigawa
Fulani sun kaurace wa wasu daga cikin manyan kasuwanin Jihar Jigawa (Dangwal Fulako), inda su kaurace wa kai dabbobi kasuwa, a yankin Masarautar Dutse. Kaurace wa kasuwar da suke yi ta fara tasiri lura da yanayin tattalin arzikin jihar, wadda mafi yawan kudin shigarta ya dogara ne da kasuwanni. Fulanin sun kaurace wa Kasuwar Sara […]
Fulani sun kaurace wa wasu daga cikin manyan kasuwanin Jihar Jigawa (Dangwal Fulako), inda su kaurace wa kai dabbobi kasuwa, a yankin Masarautar Dutse.
Kaurace wa kasuwar da suke yi ta fara tasiri lura da yanayin tattalin arzikin jihar, wadda mafi yawan kudin shigarta ya dogara ne da kasuwanni.
Fulanin sun kaurace wa Kasuwar Sara da ke Karamar Hukumar Gwaram, sun koma Kwanar Huguma a Jihar Kano, kuma sun kaurace wa Kasuwar Shuwarin da ke Karamar Hukumar Kiyawa sun koma Kasuwar Gamoji da ke Jihar Kano haka sun dauke Kasuwar Kiyawa sun kuma Miya a Jihar Bauchi.
Wannan mataki da Fulanin suka dauka ya fara tasiri ga tattalin arzikin Jihar Jigawa kuma hakan ya biyo bayan matakin da Gwamnatin Jihar ta dauka ne na raba wa manoma Dajin Yabaza a matsayin gonaki ba tare da bai wa makiyayan wajen yin kiwo ba.
Kwamashinan ’Yan sandan Jihar Bala Zama Senchi ya ce, matakin da Fulanin suka dauka na yin Dangwal Fulako don kaurace wa kasuwanni ya faru ne saboda rashin fahimtar juna a tsakaninsu da gwamnati. Ya cew umarnin da gwamnati ta bayar na a raba wa manoma Dajin Yabaza ne bai yi wa Fulanin dadi ba.
Sakamakon haka ya sa Gwamnatin Jihar ta dakatar da wancan matakin na rabon gonakin ga manoma ta umarci ’yan kwamatin rabon su sake fasalin rabon dajin kuma a tabbatar an yi wa kowa adalci.
Ya ce Gwamnatin Jihar ta kafa kwamatin da zai yi rabon dajin, domin ganin an yi wa kowanne bangare adalci wajen samar da filin kiwo ga Fulani da kuma gonaki ga manoma.