Fulani sun zargi jami’an tsaron a Jihar Filato da nuna musu bambanci

Al’ummar Fulani makiyaya da ke Jihar Filato sun zargi jami’an tsaro da nuna musu bambanci a binciken makamai da suke yi a tsakaninsu da kabilar Berom.Ardon Bachit kuma shugaban masu wa’azi da harshen Fullanci na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Malam Muhammad Bello Usman ya bayyana haka a taron manema labarai […]

Fulani sun zargi jami’an tsaron a Jihar Filato da nuna musu bambanci
Fulani sun zargi jami’an tsaron a Jihar Filato da nuna musu bambanci

Al’ummar Fulani makiyaya da ke Jihar Filato sun zargi jami’an tsaro da nuna musu bambanci a binciken makamai da suke yi a tsakaninsu da kabilar Berom.
Ardon Bachit kuma shugaban masu wa’azi da harshen Fullanci na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Malam Muhammad Bello Usman ya bayyana haka a taron manema labarai a garin Jos.
Ya ce, “Wannan bambanci da ake nuna mana mu al’ummar Fulani da sunan bincike ya kai makura. Misali kwanakin baya a yankin Ganawuri jami’an tsaro sun je sun kone mana gidaje 37 tare da kwace mana shanu da sunan suna binciken makamai. A matsayinmu na shugabanni ba a sanar da mu ba kafin a gudanar da binciken.”
Ardon ya ce an tura jami’an tsaro Mahanga da ke karamar Hukumar Riyom suka far wa Fulani suka yini suna binciken rugagensu. Ya ce amma abin mamaki suna tare da kabilar Berom ba su ga an yi musu irin wannan bincike ba, duk da suna ganinsu da bindigogi.
Ya ce ’yan kabilar Berom sun harbe musu saniya da bindiga a yankin kuma sun kai rahoto, amma ba a yi wani bincike ba. Sun sake harbe wata saniyar amma ba yi komai ba. “Wannan rashin adalci yana ba mu mamaki kwarai da gaske,” inji shi.
Ya ce “Ba mu gane laifinmu ba, shin don yawan da Allah Ya yi mana ne ko don addininmu ne ake nuna mana irin wannan bambanci? Da zarar an yi wani abu, ba tare da wani bincike ba, sai a ce Bafulatani ne sai a far mana.
Ya ce haka aka yi a yankin Keana da ke Jihar Nasarawa, inda jami’an tsaro suka tafi da motocin Hilud 15 da tankokin yaki suka je suka far wa Fulanin da ba su ji ba, ba su gani ba, suka kashe mutum 18. Sannan jami’an tsaro sun je suka yi wa Fulanin yankin Ladduga da ke Jihar Kaduna binciken kwakwaf.
Sai ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Filato da hukumomin tsaro su dakatar da wannan rashin adalci da ake nuna wa Fulani a kasar nan.
Da manema labarai suka tuntubi Kakakin Rundunar (STF) mai aikin wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato Kyaftin Ikechukwu Iweha ya musanta zargin. Ya ce ayyukan da rundunarsu ke gudanarwa a jihar suna yi ne don magance masu kawo hari a jihar. Don haka ya ce babu ruwansu da nuna bambanci kan wata al’umma ko wani mutum a aikin da suke gudanarwa.