Fulani sun zargi sojoji da cin zali da karɓar na-goro a Kaduna

Makiyayan, sun roƙi hukumomin gwamnati da su binciki lamarin tare da ɗaukar mataki kan waɗanda ake zargin.

Fulani sun zargi sojoji da cin zali da karɓar na-goro a Kaduna

Fulani Makiyaya a yankin Urban, da ke Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna, sun yi kira tare da bayyana damuwa kan zargin cin zarafi da kuma karɓar cin hanci daga wurinsu da sojojin da aka tura a ƙarƙashin aikin tsaro mai taken Operation Safe Haɓen a yankin ke yi.

Makiyayan, yayin da suke magana da jaridar Aminiya, sun roƙi hukumomin gwamnati da su binciki lamarin tare da ɗaukar mataki kan waɗanda ake zargin.

Wasu mazauna garin, waɗanda suka yi magana da wakilinmu, sun zargi wani soja mai suna Kyaftin M. Bashorun da karɓar kuɗi daga gare su domin ya saki shanun da aka kwace, tare da wasu zarge-zarge.

Muhammad Ibrahim, wani mazaunin garin Zangon Urban, ya ce ya sha fuskantar matsala da Kyaftin Bashorun, inda aka tilasta masa biyan kuɗi mai yawa don a saki shanunsa da aka kwace.

“Sojan zai ƙwace mana shanu ba tare da wani laifi ba, ya kai su sansaninsu da ke Zango, sannan sai a ce sai mun biya kuɗi kafin a sake su. A gabana ya ƙwace shanun Alhaji Goma, kuma da na tambaye shi dalilin haka, bai amsa min ba.

“Washegari, muka je sansanin sojojin don karɓar shanun, amma ya nace sai mun biya tara saboda ‘cewa Amina Sakaba ta shawarci matan da suka amfana da zakkar wannan shekara da sun lalata gona.

Mun yi ƙoƙarin cewa su (sojojin) ne suka kai shanun gonar da suka lalata, amma ba su saurare mu ba. Saboda zaman lafiya, Alhaji Goma ya bayar da kuɗin, muka biya tarar Naira dubu 140,000.

“Ba da jimawa ba bayan wannan al’amari, Kyaftin Bashorun ya sake kwace shanun, kuma ni ne na je karɓo su domin Alhaji Goma bai nan. Na nuna rashin jin daɗina kan abin da yake yi wa Fulani a wannan yankin.

“Bayan wannan, sai ga wasu sojojin ‘Military Police’ sun zo daga Jos, Jihar Filato, suna ce mana za su yi bincike kuma sun roƙi mu ba su haɗin kai.

Sojojin sun tambaye mu abin da sojojin yankin ke yi mana, kuma muka faɗa musu komai yadda ake kwace mana shanu, sannan a sake su bayan mun biya kuɗi.

“Bayan mun faɗa musu komai, suka ce mu biyo su zuwa sansanin sojojin inda ƙungiyarsu ta raba da su yi amfani da ita ta hanyar da ta dace domin dogaro da kai.

Shugabar ta shawarci matan da su yi amfani da kuɗin ta hanya huɗu yayin da ta raba musu zakkar kuɗi dubu 600 da aka bai wa mace 30 Naira dubu 20 muka maimaita abin da muka faɗa a gaban sojan da ake zargi. Bayan sun tafi, sai sojan ya yi barazanar cewa zai hukunta ni da Alhaji Goma.”

Ya ƙara da cewa, “wata rana, yayana da karnuka na suna kiwo, sai suka gamu da wannan sojan tare da wasu sojoji biyu waɗanda suke riƙe da bindigogi.

Ɗaya daga cikinsu ya harba bindiga a gefen yayana, har harsashin ya kusa shigarsa, ɗayannsu kuma ya yi harbi ya kashe ɗaya daga cikin karnuka na.

“Sakamakon tsoro, na kira wani Kanar da na sani daga Jos, na bashi labarin abin da ya faru, ya roƙe ni in tura masa bidiyon karnukan, kuma ya turawa kwamandan da ke Kafanchan. Bayan wannan, ban san abin da ya faru tsakaninsa da Kyaftin da kwamandan Kafanchan ba.

“A ranar 10 ga Satumba, 2024, sojojin sun harba bindigogi a sararin sama, sannan muka ga gidaje sun kama da wuta a kauyen kowaccensu.

“A duk sanda mutum ya samu kuɗi kar ya wuce waɗannan abubuwan guda huɗu, biyan bashi da yin jari da sayen abinci sannan ya yi sadaka. Hakan kawai zai sa ya amfani kansa da dukiyar da ya samu, duniya

Kakwa. Haka kuma, akwai wani aikin da sojoji suka yi a yankin, inda aka ƙona sbukkokin Fulani da kuma sakar shanu suka je suka lalata gonaki.

“Muna jin cewa ba mu yi wa sojoji komai ba. Na zauna tare da sojoji da dama amma ban taɓa samun matsala da su ba. Don Allah gwamnati ta shiga cikin wannan lamari,” ya roƙa.

Jafaru Salihu, Shugaban Ƙungiyar Matasa ta Bandaraku, Kaduna, ya goyi bayan labarin Ibrahim inda ya zargi wannan Kyaftin da haɗa kai da wasu mazauna yankin wajen tauye haƙƙin Fulani.

Salihu, wanda mazaunin Ladduga ne, ya ce, “Muna zauna lafiya tun bayan isowar Operation Safe Haɓen zuwa Zangon Kataf, amma abin da sojojin da aka turo don samar da zaman lafiya suke yi ba zai kawo zaman lafiya ba.

“A matsayina na shugaba, na je na ga yadda aka ƙone gidaje da idona, kuma na roƙi mutane ka da su rama, sai dai su bayyana wa duniya irin zaluncin da ake musu domin hukumomi su shiga, saboda muna son zaman lafiya. In ba haka ba, idan wani abu ya faru, za a ce Fulani ne suka kai hari, alhali ba haka ba ne.