Fulanin asali ba sa aikata ta’addanci — Sarkin Zazzau

Sarkin ya yi kira ga Fulani da su mayar da hankali wajen wanzar da zaman lafiya kamar yadda aka san su tun asali.

Fulanin asali ba sa aikata ta’addanci — Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce da zaman lafiya aka fi sanin Fulani a Najeriya ba da ayyukan ta’addanci ba.

Sarkin ya yi wannan jawabi ne a wajen wani bikin al’adu da ƙungiyar bunƙasa al’adu ta Fulani (FUDECO) ta shirya a ranar Asabar.

Bamalli, ya bayyana cewa Fulani na asali ba sa ɗaukar AK-47 don cutar da mutane.

A cewarsa, abin da ya dace shi ne, Bafulatani ya riƙe sanda da gatari don kula da dabbobinsa.

Ya kuma yi kira ga Fulani da su ci gaba da alfahari da al’adunsu da ɗabi’unsu.

Ya ce, “Ina alfahari da kasancewa Bafulatani. Kakannina duk Fulani ne, don haka dole ne na yi alfahari da gadona da al’aduna.

“Wannan taro yana taimaka mana mu gane ko mu su wane, kuma yana faɗakar da mutane game da asalin Fulani.

“Muna so mu dakatar da wannan muguwar fahimtar da ake yi game da ‘yan bindiga. Tabbas, a kowace ƙabila akwai ɓata-garin mutane, amma muna fata su daina aikata muggan ayyuka.”

Sarkin ya jaddada cewar kasancewarsa Bafulatani ba yana nufin ya ɗauki AK-47 yana aikata ta’addanci ba.

Ya ce abin da ya dace shi ne Bafulatani ya riƙe sanda da gatari, ba ya cutar da mutane ba.

Ya ƙara da cewa Fulani mutane ne masu ilimi da wayewa sosai

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja