FURE: Labarin Uwargida Farida (28)
Tun daga lokacin da aka sallamo Saratu daga asibiti ta nuna alamar cewa ta samu lafiya, wanda haka ya sanya iyayenta suka samu natsuwa. Sai dai abin da ba su sani ba shi ne, musabbabin rashin lafiyar, domin kuwa Saratu ta samu hadin kan kawarta Binta, wacce ta rufa mata asiri. Haka kuma ta samu […]
Tun daga lokacin da aka sallamo Saratu daga asibiti ta nuna alamar cewa ta samu lafiya, wanda haka ya sanya iyayenta suka samu natsuwa. Sai dai abin da ba su sani ba shi ne, musabbabin rashin lafiyar, domin kuwa Saratu ta samu hadin kan kawarta Binta, wacce ta rufa mata asiri. Haka kuma ta samu hadin kan likita Dokta KK, wanda bayan ya samu labarin abin da ya faru kuma Binta ta nemi hadin kansa domin ya rufa wa kawarta asiri ya amince.
“Shi ke nan, babu komai, Allah Ya kiyaye gaba. Ai duk wanda ya rufa wa dan uwansa asiri, shi ma Allah zai rufa nasa.” Abin da Dokta KK ya ce ke nan, a ranar da Binta ta bayyana masa matsalar kawarta. Sai dai kuma abin da ya biyo baya ya sanya kawayen biyu suka yi shakkar alkawarin da likita ya daukar musu.
Tun dazu da misalin karfe uku Binta ta ziyarci kawarta Saratu, inda suka yi ta kai-komo da al’amuran da suke ta bijiro musu. Al’amura biyu suka fi mai da hankali a kansu, tsurfar da Dokta KK ya fito da ita tun bayan da ya sallame ta daga asibitinsa sai kuma batun Alhaji Baba, wanda ya dauki lokaci bai sake waiwayarta ba.
“To shi likitan nan, wai don Allah a ganinki me yake nufi?” Saratu ta kuta, fuskarta a cakude cikin damuwa.
“Gaskiya ni kaina na rasa gane wannan al’amari,” inji Binta. “Domin kuwa shi da kansa ya gaya mini cewa zai rufa miki asiri, kuma na ga alamar haka, tun da kin ga bai fadi wa su Baba lalurar da ke damunki ba. Hasali ma ko a jikin rahotonki, abin da ya rubuta shi ne hawan jini ne lalurarki.”
kawayen sun yi shiru na dan lokaci, sun kura wa juna ido kamar kuramen da ke cikin zullumin faruwar wani abu marar kyau.
Tun da farko, Dokta KK ne ya amshi lambar wayar Saratu a lokacin da ya mika mata takardar sallama daga asibitinsa. Ya ce mata akwai maganar da zai gaya mata ne idan ta natsu a gida. Tun a ranar ya buga mata waya, daidai misalin karfe takwas na dare. Ya sanar da ita cewa yana son ta.
“Gaskiya sai dai ka yi hakuri.” Abin da ta fara gaya masa ke nan a ranar. Ta tuno da yadda ya dauki kusan minti daya bai furta komai a wayar ba, har sai da ta yi zaton cewa ko ya yi fushi ne ya kashe.
“Halo…halo…” Ta sauko da kan wayar ga fuskarta, ta duba ta ga lallai bai kashe ba, ta sake mayarwa a kunne.
“Haloooo, kana ji na?”
“Ina jin ki, amma ya kamata ki san cewa bai kamata ki nuna mini kiyayya ba. Ni na ce ina son ki kuma.” Dokta KK yana magana dalla-dalla, muryarsa cikin yanayin gargadi.
“Babu batun kiyayya a lissafin rayuwata. Ba ni da dalilin da zan nuna maka kiyayya. Abin da nake so ka fahimta shi ne, ina da alkawarin wani a kaina, wanda za mu yi aure da shi, kuma…”
“Saurara, saurara… ai kawarki ta gaya mini komai.” Bai bari ta ida maganarta ba ya shigo mata da wannan batun. “Shi saurayin naki da ya yi miki ciki, ai ya mutu ko? Ba dalili ke nan ya sa kawarki ta nemi in rufa muku asiri kada iyayenki su sani ba? To kuma wane ne kika yi wa alkawarin aure?”
“Ba za ka gane ba a yanzu Dokta,” inji Saratu, cikin muryar jan ra’ayi. “Ni dai na gaya maka cewa akwai alkawari a kaina.”
“Kada ki damu, ni dai na gaya miki ina son ki, kuma wannan ba zai shafi alkawarinki da kowa ba.” Da wannan kalami suka yi sallama da Dokta KK.
A cikin dan lokacin nan ne Saratu ta tuno da wannan sabon al’amari na Dokta KK. Kuma tun daga lokacin nan ya ci gaba da matsa mata. Har ma akwai lokacin da ya fito fili ya yi mata barazanar cewa idan ba ta yarda da shi ba, zai tona mata asiri.
“Yanzu shi yana nufin wai mu yi soyayya da shi, ba batun aure yake ba.” Saratu ta kalli Binta cikin mamaki.
“Abin da yake nufi ke nan, domin jiya ya bugo mini waya, ya ce in gaya miki wai ya samu labarin wanda kike so ki aura, Alhaji Baba.”
Saratu ta zaro idanu cikin mamaki, kirjinta na balbali. “Ke don Allah! Ta yaya aka yi ya san zancen nan?”
“Allahu a’alamu,” inji Binta. “Kin san fa duniyar nan tsukakka ce, bare ma fa kada ki manta, shi fa likitan nan na samu labarin dan duniya ne. Na samu labarin cewa tantirin dan iska ne. Ya kware wajen zubar wa mata cikin shege. Haka kuma an ce duk macen da ta kwanta asibitinsa, in dai tana da kyau sai ya nemi fasikanci da ita.”
“To ni kuwa rayuwar nan ina zan sa kaina? Matsaloli sai bijiro mini suke, daga wannan sai waccan! Ina murnar matsalar dandaula ta kwaranye sai kuma ga wata sabuwa daga Dokta, alhali ban gama daidaitawa da matsalar Alhaji Baba ba!”
“Wallahi kuwa,” inji Binta; “domin Dokta ya kama sunansa radau, ya fasalta mini inda shagonsa yake a Kantin Kwari. Ya ce in shaida miki, muddin ba ki ba shi hadin kai ba, zai san hanyar da zai lalata alakarki da shi, zai aika masa da sakamakon kwanciyarki asibitinsa…”
“karya yake! Wallahi karyarsa ta sha karya! Wallahi ba zan yarda Dokta ya yi zina da ni ba! Ya dade bai kai masa labarin nawa ba.” Saratu ta mike tsaye tana kwakwazo, har ma ta mance cewa a gidansu take. Sallamar da kanenta danliti ya yi ce ta sanya ta dawo cikin hayyacinta. Yaron ya kawo mata gyada leda, wacce ta aike shi ya sayo mata a shagon kofar gida. Bayan ya tafi ne suka ci gaba da tattaunawarsu da kawarta.
“Wallahi, wallahi rantsuwar dan Musulmi, kin san Allah sai dai kada duk rayuwata in yi aure, amma wallahi ba zan amince in yi zina da Dokta ba!” Wannan karon, cikin sassautar murya Saratu ke magana.
Za mu ci gaba