FURE: Labarin Uwargida Farida (30)
Koda Saratu ta raka kawarta bakin hanya, ba su rabu ba sai da ta samu motar A daidaita Sahu, sannan ta juyo zuwa gida. Bayan ta sallaci Isha’i, babu abin da ta yi illa nazarce-nazarcen al’amuran da suka yini suna tattaunawa da kawar tata, Binta. Kamar yadda suka tattauna, al’amura biyu ne suka bijiro wa […]
Koda Saratu ta raka kawarta bakin hanya, ba su rabu ba sai da ta samu motar A daidaita Sahu, sannan ta juyo zuwa gida. Bayan ta sallaci Isha’i, babu abin da ta yi illa nazarce-nazarcen al’amuran da suka yini suna tattaunawa da kawar tata, Binta.
Kamar yadda suka tattauna, al’amura biyu ne suka bijiro wa Saratu, wadanda kuma su ne suka zama sababbin kalubalen da take fuskanta. Akwai maganar Alhaji Baba, wanda ta riga ta gama kudurce wa zuciyarta cewa shi take so da aure. kalubalen da ke fuskantarta game da shi kuwa shi ne, yadda ya share ta, ba ya bugo mata waya kuma ba ya zuwa wurinta zance.
“Ko dazu ma da na ce Binta ta buga masa, bayan ta buga masa bai dauki wayar ba. Daga bisani ma sai ya kashe wayar.” Abin da Saratu ta fada ke nan, a lokacin da take magana ita kadai. Tana zaune a kan gado, takaici duk ya baibaiye ta.
Al’amari na biyu da suka tattauna, shi ne na batun Dokta KK, wanda ya fito mata da sabuwar tsurfa da sunan soyayya. Ta fahimce shi sosai, domin kuwa kamar yadda ya nuna, yana son ya yi amfani da sirrinta da ya sani, wajen cimma burinsa na kulla alaka da ita.
“An ce idan maye na da hankali, ba ya fid da maitarsa a fili,” inji Saratu, ta ci gaba da magana ita kadai. “To amma shi wannan likitan ga shi nan ya fito da tasa maitar fili. Ni kuwa in Allah Ya yarda, zan nuna masa cewa ba kowace mace ake yaudara ba.”
Ta buga wani uban tagumi, sannan ta jawo filo zuwa gefen kanta, a lokacin da ta kishingida. Ta ci gaba da tunanin shawarar da kawarta ta ba ta, cewa za ta raka ta zuwa wurin wani malami, wanda zai taimaka mata da rokon Allah, yadda zai shawo mata kan Alhaji Baba. Shi kuwa Dokta KK, sun saka al’amarinsa a mala da niyyar cewa za su san matakin da za su dauka a kansa.
“Maganin biri karen maguzawa. Bari in tashi in gaya wa Allah matsalolina.” Saratu ta mike tsaye, ta bar kan shimfidar da take kwance. Cikin azama ta fita waje, ta dauki buta ta daura alwala. Ta shigo dakinta, ta hau kan darduma. Ba ta gushe ba sai da ta yi raka’a biyu, sannan ta sallame. Ta kara tashi ta kawo wutiri, inda bayan ta sallame ta dauki carbi tana ta lazimi.
“Wala haula wala kuwwata, illa billahil aliyyil azim!” Abin da ta yi ta fada ke nan cikin murya mai saukin sauti. Bayan wani dogon lokaci, sai ta ji gyangyadi na rinjayarta. Ganin haka ta tsaya da jan carbin, ta daga tafukan hannayenta sama.
“Ya Allah, ba ni da karfi ba ni da iko, ba ni da dubara. Kai ne masanin boye da sarari. Ya Allah Ka iya mani, Ka san matsalolina, Ka san kasawata, Allah Ka yi mini maganin musifun da ke tunkaro ni. Ya Allah Ka karfafi niyyata, Ka daidaita al’amurana bisa shiriyarKa.” Tana gama wannan addu’a sai ta shafa. Ta mike ta bi lafiyar gado ta kwanta.
***
Da gari ya waye, kamar yadda suka shirya da kawarta Binta, daidai misalin karfe goma sha daya suka dauki hanyar Rimin Gado. Bayan sun isa, kasancewar ba su san gidan malamin ba, sai suka tambayi wani yaro da suka gani yana tallar kosai a bakin hanya.
“Ai gidansa babu nisa daga nan,” inji yaron. “Idan kuka mike wannan hanyar, ku karya kwana ta uku daga dama; gidan na nan na farko.”
“Mun gode ka ji,” inji su gaba daya, a yayin da suka ci gaba da tafiya kamar yadda ya kwatanta masu.
“Kada ki damu kawata, insha Allahu za mu dace, domin an gaya mini cewa malamin nan aikinsa kamar yankan wuka yake.” Saratu ta fadi haka da nufin kwantar da hankalin kawarta, ganin cewa kamar hankalinta a tashe yake.
“Allah Ya sa dai mutumin kirki ne, kin san fa yau wuya gare ta. Makaryata da mazambata sun yi yawa.”
Kafin wani lokaci sai ga su gaban gidan da yaron ya yi masu kwatance. A kofar gidan, sun samu wasu mutane biyu zaune a kan dakali. Suka yi masu sallama, sannan suka tambaye su mutumin da suka zo nema.
“Barkanku da zuwa ’yan mata,” inji daya daga cikin mutanen. “Ai kun zo gidan, kayanku sun tsinke a gindin kaba.” Mutumin sai ya yi zumbur ya mike, ya ci gaba da magana.
“Kun zo gidan malam jikan malam, ciki lafiya baka lafiya. Ku zo nan, ni zan yi maku iso ’yan mata.”
Mutumin nan ya jagorance su zuwa cikin zauren gidan. Ya tura kyauren wani daki da ke gefen hagu a cikin zauren.
“Ku shigo nan ciki ku zauna, zan shiga in yi maku sallama da shi.”
Saratu da Binta suka shiga dakin. Sun iske kujerin roba jingine da bangayen dakin. Ga alama dai nan ne kamar dakin da baki ke jira, kafin a yi masu iso ga malamin.
“Yanzu sai ku yi mini bayaninku daya bayan daya, yanzu zan shiga in gabatar wa malam.” Abin da mutumin ya gaya masu ke nan, amma bai bari sun fara magana ba sai ya ci gaba da nasa batun. “Za ku fadi sunayenku, daga inda kuke da kuma abin da kuke bukata. Haka kuma za ku ba da Naira dari biyar na tuntuba.”
Binta ce ta tsaya a tsanake ta yi masa bayanin duk da ya bukata. Daga bisani ta saka hannu cikin jikka ta dauko Naira dari biyar ta mika masa. Yana amsa, sai ya fita daga dakin. “Ku jira ni, zan shaida wa malam dukkan bayaninku.”
Za mu ci gaba