Furodusa Teco Benson ya caccaki Mike Ezuruonye

A kwanakin baya ne furodusan fina-finai a Kudancin najeriya, Teco Benson ya nuna bacin ransa ga dan wasa Mike Ezuruonye saboda ya gudu daga shirin fim dinsa.Kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, Mike Ezuruonye na daya daga cikin ’yan wasan da suka sanya hannun kwantaragin shirya fim din ‘Cenrifugal Force’ wanda furodusa kuma darakta Teco […]

Furodusa Teco Benson ya caccaki Mike Ezuruonye

A kwanakin baya ne furodusan fina-finai a Kudancin najeriya, Teco Benson ya nuna bacin ransa ga dan wasa Mike Ezuruonye saboda ya gudu daga shirin fim dinsa.
Kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, Mike Ezuruonye na daya daga cikin ’yan wasan da suka sanya hannun kwantaragin shirya fim din ‘Cenrifugal Force’ wanda furodusa kuma darakta Teco Benson ke shiryawa amma tun kafin a kammala daukar fim din, sai shi dan wasan ya gudu, ya ki hallara fagen daukar fim din. Wannan ya harzuka furodusan, har ya fara caccakarsa da bakaken maganganu.
“Mike ba kwararren dan wasa ba ne. A yanzu haka al’amura sun sukurkuce mana saboda kauracewar da ya yi mana, duk da cewa yana daya daga cikin jigogin ’yan wasan fim din.” Inji Teco, yana bayyana fushinsa game da kin halartar daukar fin dinsa da Mike ya yi.
Da yake kare kansa daga zargi, Mike ya bayyana cewa ba da gangan ne ya ki zuwa wajen daukar shirin ba. Ya ce ba ya da lafiya ne, ya je neman magani.
“Wannan babbar karya ce.” Inji Mike, yana kare kansa. “Ni ban kaurace wa fim din haka nan ba, ba na lafiya ne, inda kuraje suka fito mani a baki. Idan suna son ci gaba da daukar fim dinsu, za su ci gaba da wasu sassa, ba wai sai kowane dan wasa ya hallara ba. Ni ba ni da wata matsala da su kuma ya zuwa yanzu ma manajana yana magana da su domin daidaita al’amuran.”