Furodusa ya shiga tasku kan zargin damfara

An gurfanar da fitaccen furodusan fim na masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood, mai suna Uchenna Mbunabo a kotun gargajiya da ke unguwar Tinubu kan zargin damfarar jaruma Maryjane Okoye Naira miliyan daya da dubu dari bakwai.An gurfanar da Uchenna mai shekaru 28 a duniya kan zargin karbar kudin jarumar da zummar zai shirya mata fim.An […]

Furodusa ya shiga tasku kan zargin damfara

Furodusa Uchenna MbunnaboAn gurfanar da fitaccen furodusan fim na masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood, mai suna Uchenna Mbunabo a kotun gargajiya da ke unguwar Tinubu kan zargin damfarar jaruma Maryjane Okoye Naira miliyan daya da dubu dari bakwai.
An gurfanar da Uchenna mai shekaru 28 a duniya kan zargin karbar kudin jarumar da zummar zai shirya mata fim.
An zargi furodusan da karbar kudin tun watan Janairu, 2012 inda daga nan jarumar ba ta sake jin duriyarsa ba.
Lamarin ya auku ne a wurin shakatawa na bictoria Garden City da ke unguwar Ajah a Jihar Legas.
Bayan da ’yan sanda suka kama shi sai suka gurfanar da shi a gaban kotun a makon da ya gabata inda aka caje shi da aikata laifuffuka biyu na zamba cikin aminci da kuma sata.
Takardar cajin kotun ta bayyana cewa: ‘Kai Uchenna Mbunabo a wani lokaci a watan Janairun shekarar 2012 a wurin shakatawa na Garden City da ke unguwar Ajah yankin kotun gargajiya ta Tinubu ka karbi Naira miliyan daya da dubu dari bakwai a wurin Maryjone Okoye inda ka yi mata karyar za ka shirya mata fim wanda kuma ka san karya ne’.
dan sanda mai gabatar da kara Supol A. Orji ya ce laifin ya saba wa sashi na 312 karamin sashi na (1) da sashe na 285 karamin sashe na (5) da karamin sashe na (a) na kundin tsarin dokokin Jihar Legas na shekarar 2011.
Sai dai Uchenna ya musanta zargin da ake yi masa.
Alkalin kotun Misis S.K Matepo ta ba da belin wanda ake zargi a kan kudi naira dubu 500 tare da shaidu biyu da za su tsaya masa da suka mallaki adadin kudin belin.
Alkalin ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da muke ciki.