Furodusan fina-finan Indiya zai yi fim a kan wasanni
Furodusan fina-finan Indiya John Abraham wanda ya shirya fim din Madras Café zai shirya fim a kan wasanni da suka hada da kwallon kafa da tseren motoci da kuma damben boding.Ya ce: “Za mu shirya fim a kan wasanni…abin da zan iya cewa shi ne fim ne a kan kwallon kafa. A yanzu muna ci […]

Furodusan fina-finan Indiya John Abraham wanda ya shirya fim din Madras Café zai shirya fim a kan wasanni da suka hada da kwallon kafa da tseren motoci da kuma damben boding.
Ya ce: “Za mu shirya fim a kan wasanni…abin da zan iya cewa shi ne fim ne a kan kwallon kafa. A yanzu muna ci gaba da shirye-shirye, idan mun kammala za mu sanar da ranar da za mu fara daukarsa.”
“Bayan wannan akwai fina-finai biyu zuwa uku a kan sauran wasanni. Na farko tseren motoci, wanda a yanzu mun fara tsara labarin, sauran kuma a kan damben boding.” Inji shi.
Da aka tambaye shi ko zai fito a fina-finan sai ya ce a yanzu dai ba zai iya cewa komai ba, amma idan lokaci ya yi zai yi bayanin komai.
Furodusan shi ya shirya fim din ‘bicky Donor’ da kuma ‘Madars Café’, wadanda suka samu karbuwa ciki da wajen kasar Indiya