Furodusan fina-finan katun, John Dabid Wilson ya mutu

Shahararren mai shirya fina-finan katun, wato zane-zane, John Dabid Wilson, ya mutu a ranar 20 ga watan jiya.Furodusan, wanda asalinsa Baturen Ingila ne, ya mutu yana da shekaru 93 a duniya. Shi ne ya kayata fim din katun na “Lady & the Tramp,” kamar kuma yadda ya kasance wanda ya shirya gabatarwar fim din “Grease” […]

Furodusan fina-finan katun, John Dabid Wilson ya mutu
Furodusan fina-finan katun, John Dabid Wilson ya mutu

Shahararren mai shirya fina-finan katun, wato zane-zane, John Dabid Wilson, ya mutu a ranar 20 ga watan jiya.
Furodusan, wanda asalinsa Baturen Ingila ne, ya mutu yana da shekaru 93 a duniya. Shi ne ya kayata fim din katun na “Lady & the Tramp,” kamar kuma yadda ya kasance wanda ya shirya gabatarwar fim din “Grease” kuma ya yi aikin sautin fim din “The Sonny & Cher Comedy Hour” a lokacin da yake ganiyar tashensa.
John ya yi karatunsa na koyon zane-zane a hannun Dabid Hand, wanda shi ne ma ya bayar da umurni a fina-finan katun na “Snow White and the Seben Dwarfs (1937)” da “Bambi (1942)” wanda kuma shi ne ya kafa kamfanin shirya fina-finan zane-zane na “Fine Arts Films” a 1950.
Marigayin ya kware wajen shirya gajerun fina-finan katun, wadanda ba su wuce minti biyar ba. Fina-finan katun irin su “Big Yellow Tadi” da “Bad, Bad Leroy Brown” da sauransu.
Wasu daga cikin ayyukansa da suka ciri tuta, har suka jawo ya samu lambobin yabo, sun hada da fina-finansa na katun ta fuskar ilimantarwa, wadanda tashar NBC News ta rika yadawa a shekarun 1960.
An haifi marigayin a birnin Wimbledon na Ingila, a ranar 7 ga Agusta 1919. Yana dan shekara 20 ne ya shiga kungiya mai kamar soja ta “London Rifle Brigade” inda a nan ne ma har tsautsayi ya sanya ya rasa kafarsa, a sakamakon harin bam da aka kai masu a wani lokaci can baya, lokacin da suka je kasar Afrika Ta Kudu da nufin fadada yankunan mulkin mallakar Birtaniya.
Daga bisani ne ya dawo gida Landan, inda ya kama aiki a sashen zane-zane na kamfanin ‘Pinewood Studios,’ inda nan ya yi aikin zane-zanen labarin fim din ‘The Thief of Bagdad’ a 1940 da fim din ‘Great Edpectations’ a 1946. Haka kuma ya gwada kwanjin hannunsa ta fagen zane-zane a sabon kamfanin ‘G.B. Animation’ wanda J. Arthur Rank ke tafiyar da shi, wanda kuma ya yi haka ne domin ya dusasar da hasken kamfanin ‘Disney’s worldwide’ wanda shi ne ya kankane harkar fina-finan zane-zane a lokacin.
Furodusan ya mutu ya bar matarsa daya mai suna Fabian da ’ya’ya shida da kuma jikoki da dama.