Fursaunoni sun samu hutun fita zuwa gida don sabuwar shekara

Wasu ’yan kurkuku mutum dubu da 300 da ke kurkuku 300 da ke fadin kasar Sin sun samu hutun sabuwar shekara, inda suka koma gida suka hadu da ’yan uwa da iyaye, kamar yadda jami’an kula da gidajen yarin kasar da ke karkashin Ma’aikatar shari’a suka bayyana. Ma’aikatar tabayar da sanarwar ba da dadewa ba, […]

Fursaunoni sun samu hutun fita zuwa gida don sabuwar shekara

Wasu ’yan kurkuku mutum dubu da 300 da ke kurkuku 300 da ke fadin kasar Sin sun samu hutun sabuwar shekara, inda suka koma gida suka hadu da ’yan uwa da iyaye, kamar yadda jami’an kula da gidajen yarin kasar da ke karkashin Ma’aikatar shari’a suka bayyana.

Ma’aikatar tabayar da sanarwar ba da dadewa ba, cewa gidajen kurkukun kasar, wato an kyale fursunoni su ziyarci ’yan uwa da iyayensu lokacin bukukuwan sabuwar shekara, kamar yadda shafin yada labarai na cyol.com ya ruwaito.

A Shangai, fursunoni 10 daga gidajen yari hudu an ba su damar ziyartar ’yan uwa da iyaye a gidajensu, kamar yadda jami’in kula da gidan yarin ya bayyana. 

Sai dai fursunonin an gindaya musu wasu sharudda, wadanda suka hada da kyawawan dabi’u, da kammla rabin wa’adin zaman kurkuku, sannan su kasance ba su da hadari ga al’umma in sun fito waje, kamar yadda jami’in ya bayyana.

Ana bukatar su sanya Sarkar na’urar aikewa da sako lokacin fitarsu dagakurkukun, kuma da zarar sun cire sarkar ’yan sanda za su Ankara nan da nan, a cewar yadda jami’in. Kuma a kullum ’yan furdsunan sai sun rika kai wa ’yan sandan yankinsu rahoton abin da suka kasance suna aikatawa. 

Baya ga lardunan Shangai da Siuchuan da Shaandi, an kuma amince da irin wannan umarni a wasu gidajen yarin cewa ’yan uwa da iyaye za su kai ziyara a lokutan bukukuwan sabuwar shekarar, inda Sichuan ta amince akwai wa fursunoni 260 ziyara, yayin da Shaandi kuwa ya amince a kai wa fursunoni fiye da 100 irin wannan ziyara.

Dokar zamn kurkuku a kasr Sin ta daidaita hulda da ’yan uwa, inda aka kan kyale fursunoni su fice daga kurkuku don ganawa da ’yan uwa da iyaye, bayan sun cika wasu sharudda, amma bisa la’akari da kariyar hadurran da ke tattare da lamarin, tare da sauran wasu dalilai wasu gidajen yarin sun dakatar da aiwatar da irin wadannan al’amura a ‘yan shekarun nan.

Bayan gudanar da ayyukan bincike, Ministan shari’ar kasar, Zhang Jun ba da dadewa ba, ya ce gidajen yarin da ke fadin kasar za su ci gaba da aiwatar da irin wadannan ka’idoji, bayan sun yi kyakkyawan shiri da zai bayar da cikakkiyar kariya kan haduran da ke tattare da shirin.

Shirin bai wa fursunoni damar gnawa da ’yan uwa da iyaye, an dauke shi matsayin kyakkyawar ta’adar gyaran tarbiyya, kuma ma’aikatar shari’a ta fitar da tsari yadda za a ci gaba da wannan shiri a tsarin gudanar da gidajen yarin kasar.

 

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2

’Yan sanda 5 sun rasu a hatsarin mota a Kano

Tabbas ’yan Najeriya na cikin matsin rayuwa — Kalu