Fursuna ya dawo gidan yarin da ya tsere bayan shekara 30
Bayan tserewar Desic da shekara 20, jami’an shige-dafice suka daina nemansa.
Wani fursunan kasar Ostireliya wanda ya tsere daga gidan yarin da ake tsare da shi, kusan shekara 30, ya mika kansa ga mahukuntan gidan.
Bayan bullar cutar Coronavirus a bana ne fursunan ya yanke shawarar haka saboda ya rasa matsuguni kuma yana ta fama da neman aikin yi.
- ‘Babu wanda ya isa ya yi babakere a shugabancin Najeriya’
- Shekara 34 da kisan Kyaftin Thomas Sankara
A cikin daren ranar 1 ga Agustan 1992, watanni 13 a cikin shekara uku da rabi na hukuncin da aka yanke masa kan laifin shuka tabar wiwi.
Fursunan mai suna Darko Desic wanda ake kira “Dougie” ya tsere daga Cibiyar Gyara Hali ta Grafton da ke Jihar New South Wales, ta amfani da zarton yankan karfe ya balle kofofin gidan.
Kuma duk da bincike mai zurfi da hukumomi suka yi ba su iya gano inda Desic yake ba, wanda ya tsere shekara 29 baya.
Don haka, dawowarsa ta kasance abin mamaki ga kowa lokacin da ya je ofishin ’yan sanda don ya mika kansa.
Bayanai sun ce ya shiga cikin wani yanayi saboda bullar cutar ta Coronavirus, da kuma dokar kulle da aka sa a Jihar New South Wales, Desic ya rasa matsuguni kuma ba ya da hanyar da zai tallafa wa kansa.
Kafar labarai ta ABC ta ce, fursunan wanda dan asalin kasar Yugoslabia ne, ya tsere zuwa yankin bakin tekun Arewacin Sydney, inda ya yi aiki a matsayin magini.
Saboda halin da yake ciki, ya kasance koyaushe yana kiyaye kansa, bai taba yin magana da kowa ba game da abin da ya gabata, kuma yana tafiya ko’ina don neman na kansa, saboda ba zai iya samun lasisin tuki ba.
An kuma ruwaito cewa bai taba ziyartar kowane irin likita ba a cikin shekara 29 da suka gabata, don gudun kada a gano shi.
A matsayin daya daga cikin shahararrun fursunonin da suka gudu a Ostiraliya, Desic yana da dalilin guje wa ta da hankalin jama’a.
An taba nuna shi a cikin jerin shahararrun mutanen da ake nema a talabijin Ostireliya.
Tun lokacin wani mutum ya yi tunanin ya taba ganinsa a Arewacin Sydney, don haka sai ya fara kokarin ci gaba da boye sunansa.
Bayan tserewar Desic da shekara 20, jami’an shige-da-fice suka daina nemansa.
Daya daga cikin manyan abubuwan da suka sa ya tsere daga gidan yarin shi ne, fargabar idan an fitar da shi za a mai da shi zuwa kasarsa ta Yugoslabia a can kuma za a sanya shi yin aikin soja.
Yin aiki a matsayin magini yana nufin ya yi kokarin biyan kudin hayarsa, kuma yayin da ba aikin saboda barkewar annobar, lamarin ya zama mafi muni.
A wani lokaci an kore shi daga gidan da yake zaune saboda rashin biyan kudin haya, kuma an tilasta masa ya kwana a bakin teku.
A karshe, ya yanke shawarar cewa gidan yari “ya fi sauki” fiye da rashin gida don haka ya mika kansa.
A safiyar Lahadi, Darko Desic ya yanke shawarar mika kansa ga ofishin ’yan sanda na Dee Why Police Station, kuma an tuhume shi da tserewa daga gidan yari, kuma aka tsare shi a gidan yari ba tare da beli ba.
A zahiri abin da yake fata zai faru, amma yanzu jama’ar gari da ya zauna da su a cikin shekara 30 da suka gabata suna son sake ganinsa a matsayin mutum mai ’yanci.
Belle Higgins, ’yar Peter Higgins mai harkar kadarori kuma daya daga cikin manyan attajirai a cikin tekunan Arewa.
Ta fara gangamin tara kudi ta GoFundMe a yanar gizo, inda tuni ta tara sama da Dalar Amurka 25,000 (kimanin Naira miliyan 10 da dubu 306 da 250) don taimaka wa Desic mai shekara 64 gina sabuwar rayuwa.
Rahotanni sun ce, mahaifinta ya dauki wani gogaggen lauya don ya wakilci wanda ya tseren a kotu.
Sauran mutanen unguwar Desic sun yi magana a kansa sosai, suna misalta shi da mutum mai mutunci, mai aiki tukuru wanda ya tsare kansa kuma bai taba damun kowa ba.