Fursuna ya samu difloma a fannin shari’a

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wani fursuna da ke tsare a babban gidan yarin birnin Nairobi, babban birnin kasar Kenya ya karbi takardar shaidar difloma bayan da kammala karatunsa a bangaren shari’o’in dokokin al’umma daga Jami’ar birnin Landan. Fursunan mai suna Peter Ouko ya yi karatun ne daga gidan yarin ta hanyar Intanet […]

Fursuna ya samu difloma a fannin shari’a
Fursuna ya samu difloma a fannin shari’a

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wani fursuna da ke tsare a babban gidan yarin birnin Nairobi, babban birnin kasar Kenya ya karbi takardar shaidar difloma bayan da kammala karatunsa a bangaren shari’o’in dokokin al’umma daga Jami’ar birnin Landan.
Fursunan mai suna Peter Ouko ya yi karatun ne daga gidan yarin ta hanyar Intanet kuma a halin yanzu zai ci gaba da zurfafa karatunsa a fannin shari’a don neman takardar digiri.
Bikin ya samu halartar babban mai shari’a Richard Mwongo, wanda kuma ya wakilci babban jojin kasar. A lokacin wata liyafa da aka shirya masa, fursunan da wasu danginsa sun yanka wani Kek domin murnar kammala karatun.
Mahaifiyar Mista Peter wadda ita ma ta halarci bikin ta ce da ma tana da fatan dan nata ya zama Lauya kuma ta bayyana bikin kammala karatun da cewa mafarkinta ta ne ya zama gaske duk da cewa hakan ya faru ne lokacin da Peter yake gidan wakafi.
Fursunan ya ce ya ji bukatar karatun ta bijiro masa ne bayan da “alkali ya yi kuskure wajen yanke masa hukunci kan laifin kisan matarsa” da kuma yadda a yanzu zai iya taimakawa ’yan uwansa fursinoni da shawarrari kan yadda za su kare kansu a shari’ance.
Mista Peter ya shafe kimanin shekara 16 a tsare- inda da farko aka yanke masa hukuncin kisa kafin daga bisani ayi masa sassauci zuwa daurin rai-da-rai bayan kotu ta same shi da laifin a kisan mai dakinsa. Sai dai tun a wancan lokacin, Peter yake kalubalantar hukuncin kuma ana ganin samun wannan karatun zai taimaka wajen wanke kansa daga laifin.
Shugaban kungiyar agajin da ta dauki nauyin karatun, Aledander McLean, ya ce wannan na nuni da cewa gidan yari na iya zama wani waje da ke samar da ci gaba.
Akwai kuma wasu fursunoni takwas da wani mai aikin gidan yari guda da suke karatun a halin yanzu duka daga jami’ar da ke Birtaniya. Karatun na cikin jerin karatuttukan da Jami’ar Birnin Landan din take samarwa ta hanyar Intanet zuwa kasashen duniya fiye da 180, inda take da dalibai akalla guda dubu 54.
Jami’ar ita ce jami’ar da ta fi kowace tsufa wadda take ba da shaidar karatun digiri ta hanyar Intanet. Kuma daya daga cikin fursunonin da suka amfana da irin wannan karatun a baya shi ne marigayi Nelson Mandela lokacin da yake tsare a wani gidan yarin Afirka ta Kudu. Hakazalika, a lokacin Yakin Duniya na Biyu an samu dubban sojojin da ke tsare a wani sansanin fursunoni da ke kasar Jamus da suma suka amfana da irin wannan karatun.
w