Fursuna ya tsare daga kurukuku ta hanyar musaya da dan uwansa
Wani fursuna mai suna Murat mai kimanin shekara 19 da aka yanke wa hukuncin zaman gidan yarin a E Tipi Kapası a garin Mersin, da ke Kudancin kasar Turkiyya bayan samunsa da laifin kisan kai, ya tsere daga gidan ta hanyar yin musayar kamanni da dan uwansa da suke tagwaye lokacin da dan uwan mai […]
Wani fursuna mai suna Murat mai kimanin shekara 19 da aka yanke wa hukuncin zaman gidan yarin a E Tipi Kapası a garin Mersin, da ke Kudancin kasar Turkiyya bayan samunsa da laifin kisan kai, ya tsere daga gidan ta hanyar yin musayar kamanni da dan uwansa da suke tagwaye lokacin da dan uwan mai suna Huseyin, ya ziyarce shi a gidan yari.
A yayin ziyarar da Huseyin ya kai wa dan uwansa Murat, gidan yarin sun samu damar ganawa da juna wanda hakan ya ba su damar musaya da asalin wanda ke zaman gidan yarin.
A hoton da aka dauke su ba su yi kamanni da juna sosai ba a cikin gidan yarin, amma masu gadin suka fahimci ai kamanninsu daya ne don haka har suka bai wa Murat damar ficewa daga cikin gidan yarin da yake tsare.
Sai dai ba a cika samun fursunoni su yi musayar zaman gidan kaso ba saboda kamannin da suka yi, duk yawan jami’an tsaron da ke gidan yarin, a yanzu haka ana ci gaba da binciken lamarin.
Sai dai gidan yarin na E Tipi Kapası, ya fitar da rahoton cewa ba su da wata na’urar da za ta iya tantance fuskokin jama’a, amma masu gadin gidan yarin sun yi saurin fahimtar cewa, akwai wani abu da matasan suka shirya tun bayan zaman Murat, a gidan yari sama da shekara daya.
Bayan masu gadin sun gano abin da ya faru sun sanar da ’yan sandan yankin, daga nan suka fahimci cewa, tun lokacin da dan uwan Murat ya ziyarce shi a gidan yarin suka fara bincike da sauri hakan ya ba su damar cewa, Murat ya fita daga gidan yarin. A lokacin da ’yan sandan suka ziyarci gidan su Huseyin sun samu Murat a cikin gidan, daga nan suka kama shi suka mai da shi gidan yarin.
Duk tagwayen an mika su gaban kotun yayin da ’yan sanda ke ci gaba da binciken dalilin da ya sa suka yi wannan musaya tare da samun nasarar shirin da suka yi.
Wannan ne, na farko da aka taba samun tagwaye masu kama iri daya da aka samu fursuna ya yi nasarar ficewa daga cikin gidan yarin. A wasu shekaru da suka gabata akwai rahoton cewa, wani fursuna mai suna Aledander Jheferson Delgado, a kasar Peru wanda ake zarginsa da gayyatar dan uwansa da suke tagwaye zuwa gidan yarin a wancan lokacin ya samu damar ficewa daga gidan yarin ya bar dan uwansa a ciki. Bayan binciken ma’aikatan gidan yarin ta hanyar amfani da na’urar tantance yatsa sai suka fahimci cewa, wanda aka bari a ciki ba mai laifi ba ne.