Fursuna ya tsere daga kurkuku ta hanyar shigar mata
Wannan dabara da fursunan ya yi ta sa jama’a sun koma kiransa da Gordito Lindo.
A kwanakin baya ne a kasar Paraguay da ke Kudancin Amurka sunan wani mutum ya yi tambari a kafafen yada labarai.
Mutumin da ake kira César Ortiz wanda ake yi wa lakabi da Gordito Lindo, fursuna ne da ya yi nasarar fita daga gidan yari ta hanyar shigar mata.
- Nada magoya bayan Al-Bashir a mulkin Sudan na ta da kura
- NAJERIYA A YAU: Yadda Aka Yi Cinikin Kuri’a A Zaben Ekiti
César Ortiz wanda ake zargin shi ne shugaban wata kungiya ta masu aikata laifuffuka mai suna Rotela, ya tsere daga gidan yarin Tacumbú ne ta babbar kofar gidan kai-tsaye.
Gordito Lindo da har wa yau ake yi wa lakabi da “Cute Fatty,” ya canza kamanninsa zuwa mace ce don yaudarar masu gadin gidan yarin.
Hotuna da bidiyo da hukumomin kasar Paraguay suka fitar sun nuna wanda ake zargin sanye da dogon gashi a kai da gashin gira na jabu da jambaki da farce na bogi da sauran kayan mata.
Dabarar da fursunan ya yi ta janyo jama’a suna cewa lakabin na Gordito Lindo ya dace da shi.
Ortiz ya samu dabarar tserewa ya shiga wani daki na wata mata sannan ya fita sanye da gyale da kayan mata da ya yi nasarar yaudarar masu gadi a shingayen bincike da dama.
A cikin wani hoton bidiyo da ya rika karade Intanet, an gan shi yana fita ta babbar kofar gidan yarin dauke da jakunkuna da dama sanye da takunkumin rufe fuska.
Kodayake tserewa daga gidan yari da Gordito Lindo ya yi ta fi sauki fiye da yadda yake tsammani, sai dai samun ’yancinsa bai dade ba, yayin da ’yan sanda suka kama shi bayan sa’o’i kadan.
Yanzu haka an maida shi gidan yarin kuma an shirya sauya masa wani gidan yarin saboda dalilan tsaro.
César Ortiz yana zaman gidan yari na shekara uku da wata tara da kwana 20, saboda mumunan hari da fashi da makami da ya kai.
Mai yiwuwa ne hukuncin nasa ya karu bayan faruwar wannan lamari.
A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike daga gidan yari cikin sauki da ya yi, kuma tuni aka dakatar da jami’an tsaro da ke bakin aiki a babbar kofar shiga gidan yari na Tacumbú.
Wannan ba shi ne karo na farko na tserewar fursuna a kurkuku da aka taba wallafawa ba.
A shekarun baya, mun yi rahoto kan wani fursuna da ya yi kokarin fita daga gidan yari ta hanyar buya a cikin akwati inda budurwarsa da ta ziyarce shi ta dauke shi.
Daga nan sai mutumin da ya yi kama da ’yars da kuma wani dan kasar Turkiyya wanda ya sauya zaman furuna da dan uwansa da suke tagwaye.