Fursunan da aka daure rai da rai ya kammala karatun digiri a kurkuku
Wani fursuna mai matsakacin shekaru mai suna Tunwase Kabiru da ke zaman rai da dai a kurkukun kirikiri da ke Legas ya kammala karatun digirinsa na farko lokacin da yake tsare.Tuwanse ya kammala karatun ne tare da dalibai dubu hudu da 308 da suka yi karatu a karkashin Jami’ar Karatu Daga Gida (National Open Unibersity […]

Wani fursuna mai matsakacin shekaru mai suna Tunwase Kabiru da ke zaman rai da dai a kurkukun kirikiri da ke Legas ya kammala karatun digirinsa na farko lokacin da yake tsare.
Tuwanse ya kammala karatun ne tare da dalibai dubu hudu da 308 da suka yi karatu a karkashin Jami’ar Karatu Daga Gida (National Open Unibersity of Nigeria -NOUN).
An mika wa Kabiru takardar shaidar digirinsa kan Gudanar da Harkokin Ma’aikata, inda ya samu rakiyar jami’an kurkukun zuwa wurin bikin saukar karatun daliban jami’ar a Legas.
Ya shaida wa Kamfanin DillancinLabarai na Najeriya (NAN) yanzu haka yana zaman daurin rai da rai ne a kurkuku a kirikiri ne sakamakon samunsa da laifin kisan kai.
Ya ce “Ina yi wa Allah godiya a kan abubuwan da Yake yi min a rayuwata. Kullum ina fatan samun alheri daga Ubangijina, kuma wannan ne ya karfafa min gwiwa na shig makarantar. An daure ni bayan an same ni da alhakin kisan kai kuma na shafe shekara 11 a kurkuku. Ina tsammanin abubuwa za su sauya wata rana in samu kyakkyawar rayuwa lura da nasarar da na samu a yau.”
Matamakin Kwanturola Janar na Hukumar Kurkuku ta kasa, Chuks Afejue ya yaba karfin zuciyar fursunan inda ya ce shi ne na farko da aka dauka ya far karatu a cibiyar karatu ta kurkukun.
A cewar Afejue wannan zai nuna wa mutane cewa yanzu kurkuku ba jujin ajiye wadanda suka yanke kauna ba ne.
Ya ce “Kurkuku wuri ne na gyara hali. Kuma a yanzu haka muna da fursunoni 48 da suke irin wadannan cibiyoyi guda hudu na gidajen yarin da suke sassan kasar nan. Abu ne mai faranta rai, kuma muna son yin amfani da wannan dama wajen rokon Gwamnatin Tarayya ta yi masa jin kai, ganin nasarar da ya samu.”
Daraktan Cibiyar Karatun Malam Ladan Baba Kwadon ya ce wasu fursunoni biyu da ya kamata su kamala karatu tare da Kabiru, su gaza yin haka saboda rashin samun sakamakon da ya kamata.
Ya ce bincike ya nuna kwazon fursunonin ya dara na sauran takwarorinsu da ke waje, saboda aikin da suke yi kawain a kurkukun shi ne karatu.