Fursunoni 52 sun zana jarabawar kammala sakandare a Kano
Kwamturolan hukumar ya ce wannan wani mataki ne na bai wa fursunonin damar samun ilimi.
Fursunoni 52 da ke gidajen gyaran hali daban-daban a Jihar Kano sun fara rubuta jarabawar kammala sakandare ta NECO da NABAIS ta shekarar 2026.
Masu rubuta jarabawar sun haɗa da maza 41 da mata 11, waɗanda aka zaɓo daga gidajen gyaran hali daban-daban a jihar.
Wannan na daga cikin shirin Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa na bai wa fursunoni ilimi domin gyara rayuwarsu da kuma taimaka musu su koma cikin al’umma bayan sun kammala zaman gidan gyaran hali.
Mai magana da yawun hukumar a Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nassarawa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.
Sanarwar ta ce Kwanturolan Gidajen Gyaran Hali na Jihar Kano, Yusuf Ahmad Lakpene, ya ziyarci cibiyoyin da ake zana jarabawar domin duba yadda aka fara gudanar da ita.
Lakpene, ya ce shirya wa fursunoni irin wannan jarabawa wani muhimmin mataki ne na gyara halinsu da ba su damar samun ilimi da zai amfani rayuwarsu a gaba.
Ya kuma buƙaci masu rubuta jarabawar su kasance masu gaskiya da bin ƙa’idoji, yana mai cewa ilimi na taimaka wa mutum ya sauya rayuwarsa kuma ya zama ɗan ƙasa na gari.
Hakazalika, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano, bisa biyan kuɗin rajistar jarabawar fursunonin, yana cewa hakan ya nuna gwamnati na bai wa kowa damar samun ilimi, har da waɗanda ke gidajen gyaran hali.
Ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da faɗaɗa shirye-shiryen ilimi a gidajen gyaran hali domin taimaka wa fursunoni su samu ilimi da kuma gyara rayuwarsu.