Fursunoni sun tsere daga gidan kaso a Sudan
Jami’an sun hadar da Ahmed Haroun da ke tsare tare da tsohon Shugaban Kasar, Omar al Bashir
Rahotanni na cewa wasu tsoffin jami’an gwamnatin Sudan da karin wasu fursunoni sun tsere daga gidan kason da ake tsare da su.
Lamarin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin masu biyayya ga gwamnati da dakarun RSF duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma bisa jagorancin Amurka.
- Manchester United za ta yi wa Harry Kane tayi mai gwabi
- Zaben Adamawa: Kotu ta kori karar da Binani ta shigar
Jami’an sun hadar da Ahmed Haroun da ke tsare tare da tsohon Shugaban Kasar, Omar al Bashir wadanda su duka biyu kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ke nema ruwa a jallo bisa aikata laifin kisan bil’adama a Darfur.
A wani faifan bidiyo da gidan talabijin din Sudan ya watsa ya nuno Ahmed Haroun din yana cewa sun share kwanaki tara ne a tsare a gidan kason na Kober da ke Khartum kafin su yi ta ransu sakamakon zafafar hare-hare a kusa da inda suke kuma a halin yanzu suna a guri marar hadari.
To sai dai a daren jiya Talata Gwamnatin Sojin Sudan din ta sanar da cewa tsohon shugaban kasar Omar al Bashir da aka hambarar a shekarar 2019 na ci gaba da jinya a wani asibiti bisa sa idon jami’an tsaro.
Kazalika, ta ce ana binciken gano inda Ahmed Haroun din wanda ke da hannu a yakin basasan Darfour ya buya.
Mayakan RSF sun kwace matatar man fetur ta Sudan
Dakarun RSF da ke yakin neman iko da sojojin Sudan sun yi ikirarin karbe iko da matatar man fetur ta asar, wadda ke da nisan kilomita 70 daga Arewacin birnin Khartoum, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.
AFP ya ce RSF sun yi wannan ikirari ne cikin wani bidiyo wanda ciki suka ce sun kwace iko da tashar lantarki ta Garri.
A ranar Talata, rundunar sojin kasar cikin wani bayani da ta wallafa a Facebook ta yi gargadin cewa, “wata babbar tawaga mayaka ta nufi matatar”, a wani mataki na amfani da damar tsagaita wutar domin kwace iko da tashar lantarkin.