Furta sunan ‘Allah’ ya sa ana zargin dan shekara shida da ta’addanci

Ana zargin yaro dan sshekara shida mai cutar dukum da aikata ta’addanci, inda malaminsa ya kirawo ’yan sanda lokacin da yaro ya rikka maimaita Kalmar “Allah” a ajinsa, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito. Ya ce asalin malamin da yake koyar da dansa karatu a makarantar Elemantare ya bar makarantar don haka aka kawo […]

Furta sunan ‘Allah’ ya sa ana zargin dan shekara shida da ta’addanci

Ana zargin yaro dan sshekara shida mai cutar dukum da aikata ta’addanci, inda malaminsa ya kirawo ’yan sanda lokacin da yaro ya rikka maimaita Kalmar “Allah” a ajinsa, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.

Ya ce asalin malamin da yake koyar da dansa karatu a makarantar Elemantare ya bar makarantar don haka aka kawo wani malamin, wanda ya kira masa ’yan sandan Pearland, kimanin kilo,mita 32 a Kudancin Houston da ke Jihar Tedas

Shi kuwa malamin ya tabbatar wajami’an ’yan sanda cewa Mohammad ya iya magana.Cikin takaicin wannan zargi, mahaifin Mohammad ya jajirce kan cewa dansa ba ya iya yin magana, kuma kwakwlwarsa tamkar ta yaro dan shekara guda take, kamar yadda jaridar The Independent ta ruwaito.

“Sun yi ikrarin cewa shi dan ta’adda ne. Wannan shirrmee ne, kuma nuna wariya ne a hakikanin gaskiya. 

Ba ma ayyana wariyar kawai aka yi ba, har ma an tabbatar da ita dari bisa dari,” inji mahaifin.

’Yan sandan Pearland sun ce sun kammala bincikensu amma ba su samu wani laifi a tattare da shi ba, don haka ba a bukatar daukar wani mataki.

Sai dai Hukumar kare hakkin yara ta ce tana ci gaba da binciken lamarin.

Irin wadannan al’amura na zargin nuna wariya ga Musulmi sun auku ne a Jihar Tedas ta Amurka.