Furucin TY Danjuma tamkar kiran tashin hankali ne-Gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya ta bayyana kiran da tsohon ministan tsaro, Laftanar Janar, Theophilus Yakubu Danjuma ya yi na kiran jama’a su tashi su kare kansu da tamkar kiran a yi tashin hankali. Danjuma wanda shi ne tsohon shugaban rundunar sojoji ya yi furucin ne a taron bikin yaye daliban jami’ar jihar Taraba a ranar Asabar […]
Gwamnatin tarayya ta bayyana kiran da tsohon ministan tsaro, Laftanar Janar, Theophilus Yakubu Danjuma ya yi na kiran jama’a su tashi su kare kansu da tamkar kiran a yi tashin hankali.
Danjuma wanda shi ne tsohon shugaban rundunar sojoji ya yi furucin ne a taron bikin yaye daliban jami’ar jihar Taraba a ranar Asabar din da ta gabata inda ya zargi rundunar sojan Najeriya da daukar matsayi a fadan fulani makiyaya da manoma.
A sanarwar da ya sanyawa hannu, Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali ya ce “Rundunar sojan Najeriya a tsare take kuma kwararru ne wajen gudanar da aiyukansu kamar yadda kundin dokokin Najeriya ya tanada”.
Sanarwar Ministan wacce mai magana da yawunsa, Kanar Tukur Gusau ya fitar ya yi kira ga dukkan wanda yake da wata hujja da ke nuna take doka da sojoji suka yi da ya bi hanyoyin da aka tanada don gabatar da hujjojinsa.