Fushi da mata
Wani matashi ne ya fito waje, domin matarsa ta bata masa rai, ashe bai sani ba shi ma innarsa ta bata wa babansa rai kuma a daidai lokacin bai san cewa baban nasa yana bayansa ba. Matashin nan sai ya ce: “Allah Ka la’anci mata amma ban da innata.” Jin haka sai babansa ya yi […]
Wani matashi ne ya fito waje, domin matarsa ta bata masa rai, ashe bai sani ba shi ma innarsa ta bata wa babansa rai kuma a daidai lokacin bai san cewa baban nasa yana bayansa ba. Matashin nan sai ya ce: “Allah Ka la’anci mata amma ban da innata.” Jin haka sai babansa ya yi wuf cikin fushi ya ce: “Hada da ita Allah, ai ita ce ma babbar la’ananna.”
Daga Amiru Isa Bakori, 08075959086