Fuskokin Limaman Sallar Tarawih da Tahajjud a Makkah
Manyan limamai da aka zabo don jagorantar sallolin dare a watan Ramadan, 2021
Hukumomin Saudiyya sun fitar da jerin sunayen limaman da za su jagoranci Sallolin Taraweeh da na Tahajjud a Masallaci mai alfarma na birnin Makkah a cikin watan Azumin Ramalana mai kamawa.
Shafin intanet na Haramain Sharidain ya sanar cewar limamai shida ne za su jagorancin sallolin a tsawon watan Azumin bana, karkashin jagorancin Sheikh Abdurrahman As Sudais, Babban Limamin Masallatai biyu mafiya alfarma a doron kasa na Makkah da Madinah.
- Ranar Tarin Fuka: Ganduje ya yi gargadi kan amfani da magungunan gargajiya
- Coronavirus ta kashe mutum 300,000 a Brazil
Limaman su ne Sauran su ne;
- Sheikh Saud Al Shuraim
- Sheikh Abdullah Awad Al Juhany
- Sheikh Maher Al Muaiqly
- Sheikh Bandar Baleelah da kuma
- Sheikh Yasir Al Dossary.
Kazalika, sanarwar ta ce a bana babu wani limami daga wani masallaci da za a gayyato domin jagorantar sallolin.