Fuskokin ’yan Boko Haram na kara bayyana
Kafin fallasar da Steben Dabis ya yi a makon shekaranjiya cewa tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff da tsohon Babban Hafsan Sojojin kasa, Laftana Janar Azubuike Ihejirika na daga cikin masu tallafa wa ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram, wasu masana da suka hada da wata Ba’amurkiya mai suna Farsfesa Jean Herskobits da […]
Kafin fallasar da Steben Dabis ya yi a makon shekaranjiya cewa tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff da tsohon Babban Hafsan Sojojin kasa, Laftana Janar Azubuike Ihejirika na daga cikin masu tallafa wa ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram, wasu masana da suka hada da wata Ba’amurkiya mai suna Farsfesa Jean Herskobits da wani tsohon jami’in leken asiri dan kasar Ingila mai suna Gordon Duff wanda yanzu ya zama dan jarida sun bayyana cewa matsalar Boko Haram, matsala ce da akwai hannun ’yan siyasa da jami’an tsaro da kasashen waje da kamfanoni masu sayar da makami da abokan adawa da kuma ita kanta gwamnatin Najeriya.
Farsfesa Jean Herskobits a wani rubutunta da jaridar New York Times ta buga a ranar 2 ga Janairun 2012 ta ce ba Boko Haram ne matsalar hare-haren da ake kaiwa a nan Najeriya. Shi kuma Gordon Duff a rubutun da ya yi a jaridar betran, ta ranar 14 ga Nuwamban, 2011 mai taken: “An shirya wargaza Najeriya ya lissafo bangarorin da suke cin gajiyar lamarin ta fakewa da Boko Haram domin cimma wasu manufofi.
Dukkan Turawan biyu sun san Najeriya sosai, ita Farfesar wakiliya ce ma a Gidauniyar TY danjuma, yayin da Duff ya yi aikin leken asiri na tsawon shekara 20 a Najeriya. A rubutun Duff ya ce: “Babu wata niyya ta gaskiya domin dakile ayyukan Boko Haram, saboda dimbin bukatu na wasu gwamnatocin kasasehn waje da hadin bakin wakilansu da ke cikin gwamnati mai ci a Najeriya da ita kanta kasar. Ga wasu da ke cikin gwamnati, Boko Haram ta zama wani makami ne na juya wasu daidaikun mutane.”
Ya kuma ce an rika amfani da Boko Haram domin jan hankali, misali ‘A kashe “Wasu ’yan Najeriya,” ko “Kiristoci,” domin a nuna kamar fada ne a tsakanin Kiristanci da Musulunci domin a tunzura ’yan Najeriya. Idan ba su harzuka ba, a sake kashe wasu ko a farmaki wasu fitattu domin a samar da kanun labarai a jaridu.”
Bayan wadannan masana tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Janar Andrew Azazi ya dora alhakin hare-haren bam da ake jinginawa ga Boko Haram a kan Jam’iyyar PDP, bayanin da ake zargin shi ne ya jawo ajalinsa.
Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako wanda tsohon soja ne ya zargi gwamnati da sojoji da hannu a harkar Boko Haram, bayanin da ya jawo masa rasa kujerarsa. Sannan Sheikh Ibrahim Zakzaky ya ce gwamnati ce Boko Haram, shi ma ya jawo rasa ’ya’yansa uku da almajiransa 30.
Janar Buhari ya ce gwamnatin Najeriya ita ce babbar ’yar Boko Haram, ya yi kusan rasa ransa, Sheikh dahiru Bauchi ya ce wasu jami’an gwamnati na cin gajiyar matsalar Boko Haram, shi ma ya yi kusan rasa ransa. Shugaban kasa da kansa ya shaida wa duniya cewa akwai ‘’yan Boko Haram a cikin ministocinsa.
Wadannan abubuwa da suke faruwa sun tabbatar da cewa lallai akwai kanshin gaskiya kan bayanan da Turawan nan biyu suka na cewa akwai fuskoki da dama a cikin harkar Boko Haram.
Amma babu wanda ya fara fitowa da fuskokinsu a fili duniya ta gani irin Rabaran Steben Dabis.
Fallasar da Rabaran Dabis ya yi ta sa a ranar Juma’ar da ta gabata, jaridar Premium Times da ke fitowa a intanet ta saki wani rahoton sirri da sake alakanta tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff da Shugaban kasar Chadi, Idris Derby da hannun su a harkar Boko Haram. Kuma kwatsam ranar Litinin sai ga labarin an kama wasu ’yan Najeriya biyu da wani Bayahude dan kasar Isra’ila mai suna Eyal Mesika a kasar Afirka ta Kudu dauke da tsabar kudi Dalar Amurka miliyan tara da dubu 300 (kimanin Naira biliyan daya da miliyan 534 da dubu 500) sun je sayo makamai da sunan gwamnatin Najeriya. Kuma bayanai sun ce jirgin da suka je sayo makaman da shi mallakar Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya ne (CAN), Fasto Ayo Oritsejafor.
An kama masu sumogal makaman ne bayan sun sauka a filin jirgin saman Lanseria International Airport da ke birnin Johannesburg ranar 5 ga Satumban nan a cikin jirgin da ya tashi daga Abuja dauke da jakunkuna uku makare da Dalolin kamar yadda wata jaridar Afirka ta Kudu mai suna City Press, ta ruwaito.
Kakakin Hukumar Tara Kudin Shiga ta Afirka ta Kudu (SARS), Adrian Lackay ta tabbatar da cewa ma’aikatan kwastam sun sha jinin jikinsu lokacin da fasinjojin jirgin suke sauka da jakunkunansu kamar yadda jaridar ta bayyana, inda aka sanya su a na’urar duba kayan da suke dauke da su.
Kuma abin mamaki sai ga shi gwamnatin Najeriya ta amsa cewa kudin nata ne! Fasto Ayo Oritsejafor ya amince jirgin nasa ne! Me za a yi da makaman da za a sayo? Makaman na wane ne? Shin haka dama ake yi wajen sayo makamai tsakanin kasashen duniya?
Idan muka takaita abubuwan da suka faru a ’yan kwanakin nan kawai za mu amince da bayanan da ke cewa akwai hannun:
1.’Yan siyasa a Boko Haram- wadanda Ali Modu Sheriff ke wakilta.
2. Hannun gwamnati da sojoji – wadanda Janar Ihejirika ke wakilta.
3. Hannun Kiristoci – wadanda Fasto Oritsejafor ke wakilta.
4. ’Yan Boko Haram na ainihi a karkashin Abubakar Shekau.
Sai dai abin tambaya wane ne zai tabbatar da wannan zargi ko akasinsa? Gwamnati wadda ita ya kamata ta bincika don gano masu hannu a cikin wannan aikin assha da Allah wadai, ita kanta abar zargi ce. Kuma ta nuna hakan yadda ta hanzarta wanke Janar Ihejirika da kuma yadda Shugaban kasa ya tafi kasar Chadi da Sanata Ali Modu Sheriff wadanda Rabaran Dabis ya zarga da hannu a tallafa wa Boko Haram.
Ita dai jaridar Premium Times da ta ruwaito cewa tana da bayanan sirrin da ta samu a Maiduguri da Damaturu da Abuja da suka nuna ranakun da aka yi musayar bayanan sirri a tsakanin hukumomin soja sun nuna yadda aka samu hannun Sheriff a cikin harkar horar da ‘’yan Boko Haram a garin Abeche da ke kasar Chadi. Kuma ta gano hadin baki da goyon bayan Shugaban Chadi da jami’an gwamnatin Najeriya da Jamhuriyar Nijar a karkashin kai-kawon SAS.
Abu na baya bayan nan da ke nuna akwai wata muguwar manufa da ake son cimmawa da sunan Boko Haram, shi ne yadda ba kunya ba tsoron Allah Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Dabid Mark ya fito ya shaida wa duniya cewa “Zaben badi bai cikin abin da suke tunani a yanzu,” saboda kasar nan tana yaki da Boko Haram.
Me zai hana mu yi tambayar cewa anya ba wani shiri ne na tazarce ga Shugaba Jonathan ba ya ake ta kai hare-hare da sunan Boko Haram kuma a ce sojojin kasar nan sun kasa murkushe su?
Ya kamata Dabid Mark ya fahimci cewa hatta a Sriya da Iraki da Somaliya da suke cikin tsakiyar yaki shekara da shekaru kuma sassa da dama na kasashen ba su karkashin ikon gwamnati ana gudanar da zabe, balle Najeriya.
Ga ’yan Najeriya, Musulmi da Kirista, mu ci gaba da addu’o’in Allah Ya fallasa masu hannu a harkar Boko Haram kuma Ya tozarta su, kada mu gajiya musamman a yanzu da aka fara hasko mana fuskokinsu