Fyaɗe ya yi sanadin mutuwar ‘yar shekara biyu a Bauchi

Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta bayyana cewa, an yi wa wata yarinya ’yar shekara biyu fyaɗe har lahira a Ƙaramar Hukumar Ningi ta Jihar Bauchi. Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Mohammed Wakil a wata sanarwa da ya raba wa manemalabarai a ranar Talata, inda ya ce lamarin ya […]

Fyaɗe ya yi sanadin mutuwar ‘yar shekara biyu a Bauchi

Kotu

Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta bayyana cewa, an yi wa wata yarinya ’yar shekara biyu fyaɗe har lahira a Ƙaramar Hukumar Ningi ta Jihar Bauchi.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Mohammed Wakil a wata sanarwa da ya raba wa manemalabarai a ranar Talata, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar 5 ga Nuwamban 2024.

Ya ce, an kai rahoton aikata laifin ne a hedikwatar ‘yan sanda ta Ningi. “An gano gawar wata jaririya wani masallaci da ke kan titin Deneva, a Ƙaramar Hukumar Ningi da alamun fyaɗe aka yi mata,” in ji shi.

“Bayan samun rahoton an aika jami’an tsaro zuwa wurin, inda suka ɗauko gawar kuma zuwa babban asibitin Ningi, inda rahoton likita ya tabbatar da cewa jaririyar ta samu munanan raunuka sakamakon kutsawa da aka yi cikin farjinta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta.”

Kwamishinan ‘yan sanda, Auwal Musa Mohammed ya yi Allah-wadai da lamarin, inda ya bayyana shi a. Wakilin inmu ya bayyana cewa, Kwamishinan ’yan sandan ya umarci jami’in ’yan sandan da ke kula da shiyyar Ningi da su yi ƙoƙarin kamo waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya.

Ya kuma yi kira ga iyaye da masu kulawa da su tabbatar da tsaron ’ya’yansu, kar su bari su riƙa yawo a kan tituna.

Kakakin ya ƙara da cewa, “Rundunar tana neman taimakon jama’a da duk wani bayani mai amfani da zai taimaka wajen kamawa da hukunta waɗanda suka aikata laifin.”

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Tags