Fyade: An yanke wa maza biyar daurin rai da rai a Masar

Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa wasu maza biyar hukuncin daurin rai da rai, bisa samunsu da laifin aikata lalata da wasu mata.Haka kuma kotun ta yanke hukuncin dauri na tsawon lokaci ga wasu mazan biyu da aka samu da laifin yunkurin yin fyade da kisa da kuma azabtarwa.A lokacin bikin rantsar da […]

Fyade: An yanke wa maza biyar daurin rai da rai a Masar
Fyade: An yanke wa maza biyar daurin rai da rai a Masar

Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa wasu maza biyar hukuncin daurin rai da rai, bisa samunsu da laifin aikata lalata da wasu mata.
Haka kuma kotun ta yanke hukuncin dauri na tsawon lokaci ga wasu mazan biyu da aka samu da laifin yunkurin yin fyade da kisa da kuma azabtarwa.
A lokacin bikin rantsar da sabon Shugaban kasar Masar Abdul Fattah al-Sisi ne aka yi lalata da matan.
Masu aiko da rahotanni sun ce hukuncin zai dan rage damuwar da ake nunawa game da gazawar hukumomi wajen magance matsalar cin zarafin mata a kasar.