Fyade: An yi wa dan shekara 60 daurin rai-da-rai
An yi wa mai shekara 60 daurin rai-da-rai saboda yi wa ’yar shekara 9 fyade
Kotu ta yi wa wani tsoho mai shekara 60 daurin rai-da-rai saboda yi wa ’yar shekara 9 fyade.
An yi wa wani tsoho mai shekaru 60 daurin dai-dai rai bisa laifin yin lalata da karamar yarinya mai shekara tara a Jihar Jigawa.
- Uba ya ba ’yar cikinsa kwaya, ya yi mata fyade a Ogun
- Kotu ta yanke wa masu garkuwa da mutane daurin shekara 36
An gurfanar da tsohon ne a gaban wata babbar kotu da ke zaune a Dutse, babban birnin jihar, bisa zargin sa da yaudarar wata yarinya mai shekara tara da kuma yi mata fyade a gidansa da ke kauyen Doro da ke karamar hukumar Jahun.
Alkalin kotun, Mai shari’a A.M Sambo ya ce laifin fyade ya saba wa sashe na 282(1) (e) na dokar Penal Code na Jihar Jigawa na shekarar 2012 da kuma hukunci a karkashin sashe na 3 na kundin laifuffuka.
Wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin da ake zargin sa da aikatawa.
Sai dai lauyan mai shigar da kara, ya gabatar da shaidu tare da gabatar da hujjoji guda biyu, ciki har da rubutaccen bayanin wanda ake zargin a hannun ’yan sanda da kuma rahoton likita don tabbatar da kararsa.
Ya ce laifin fyaden yana da hukuncin daurin rai-da-rai idan aka same shi da laifi.
Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Sambo ya ce lauyan masu shigar da kara ya tabbatar da kararsa ba tare da wata shakka ba, don haka ta yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin daurin rai-da-rai.