Fyade da kisan matan aure: ina mafita?

Ga masu bibiyar kafafen watsa labarai sun ji yadda wata bakuwar al’ada da ta kunno-kai cikin al’ummar Hausa -Fulani, a inda ake samun wasu bata gari da ‘yan ta-more suna tsallakawa gidaje, su yi wa sababbin amare fyade, tare da kashe su. Wannan wani abu ne mai matukar tayar da hankalin dukkanin mutumin da yake […]

Fyade da kisan matan aure: ina mafita?
Fyade da kisan matan aure: ina mafita?

Ga masu bibiyar kafafen watsa labarai sun ji yadda wata bakuwar al’ada da ta kunno-kai cikin al’ummar Hausa -Fulani, a inda ake samun wasu bata gari da ‘yan ta-more suna tsallakawa gidaje, su yi wa sababbin amare fyade, tare da kashe su. Wannan wani abu ne mai matukar tayar da hankalin dukkanin mutumin da yake da imani da tausayi a cikin zuciyarsa. A lokutan baya abu ne mai matukar wahala ka ji irin wannan mummunan al’amari ya afku, amma ko a kwanan nan sau biyu ke nan irin hakan tana faruwa a Jihar Kano, jihar da aka santa da kokarin bin addini sau da kafa.
To, mene ne ya jawo mana wannan bakon al’amari? A nan na yi nazarin wasu daga cikin abubuwan da nike ganin su ne suke haddasa wannan al’amari, wanda nike fatan su ma al’ummar gari da hukumomin tsaro za su tsaya su yi nazari akan abubuwan da suke haddasawa, tare da neman mafita don samun kwanciyar hankali. Domin kuwa abin ya fi karfin a tsaya ana tunanin hukuma ce za ta magance, a’a sai mun hada karfi da karfe, sannan mun zage damtse wajen rokon Allah ya magance mana wannan bala’i.  
Abubuwa da yawa ne suka haddasa wannan al’amari, amma ga kadan daga ciki; na farko dai shi ne; tara samari barkatai: mafiya yawancin masu aikata irin wannan ta’annati sun san matan (da suke yi wa fyaden) tun kafin a yi musu aure, abin da nike nufi a nan shi ne; akwai wata al’ada da mu ‘yan matan wannan zamani muka farar da ita wajen tara samari iri-iri, kai za ka ga wasu ma har sunaye suke rada wa samarinsu; wani ATM, wanda aikinsa kawai, shi ne, duk lokacin da ake bukatar kudi shi za a tuntuba, wanda hakan ba karamar matsala take jawowa ga ‘yan uwana mata ba. Domin kuwa idan kin ci kudin wani ya yi hakuri, wani fa wallahi ko ta halin kaka sai ya fanshe kudinsa!. Haka kuma wasu matan bayan sun gama tatse samarin, sai kuma su rabu da su ta hanyar cin mutumci da wulakanci iri-iri.
Na biyu, kafofin sada zumunta na facebook da whatsapp da tweeter da dai sauransu. Wannan ma wata hanya ce da ‘yan uwana mata (na aure da ‘yan mata) suka tsunduma ka’in da na’in suna yinta babu kakkautawa. Wani abin haushin ma, shi ne, za ki samu idan mace tana amfani da wadannan kafofi da na ambata a sama, to, sai ta zabo hotunanta wadanda suka fi kyau, ta fito da dukkanin lungu sakon da yake jikinta, sannan za ta yi Posting, to, idan wadannan miyagun suka gani haka za su yi ta yaudarar mace da hira mai dadi, ta haka har ya samu ya yaudareta, matsalar da ake samu a nan shi ne kin rubuta dukkanin bayanan da suka shafe ki, wanda hakan yana saukaka hanyoyin da za a gano adireshinki da dukkanin wadansu muhimman bayanai da mugu zai bukata domin ya aiwatar da mummunan kudurinsa akanki.
Na uku; Shaye-shayen miyagun kwayoyi ya yawaita matuka a cikin garuruwanmu, wanda kamar yadda Annabi Muhammad, tsira da aminci su kara tabbata a gare shi; ya ce: “Giya ce uwar dukkanin wani mugun aiki”. Giya a nan yana nufin dukkanin abin da idan ka/ki sha zai gusar miki da hankali. Haka kuwa abin yake domin kusan daukacin wadanda suke aikata wannan aiki na fyade za ka samu sai sun bugu (da kayan maye, sawun giyar d aaka sani ko kwaya ko tabar wiwi da saurn su) suke aikatawa.
Yadda za a magance wannan matsalar  kuwa, ita ce; iyaye su sanya ido akan wadanda suke zuwa zance (tadi) wajen ‘ya’yan su mata. A duk lokacin da uba ko wakilinsa ya ga ‘yarsa da wani suna zance, to, lallai ya binciki daga ina ya zo kuma su wane ne iyayensa. Sannan bayan an zabar mata miji, to, dole a hanata mu’amala da kowa domin gudun fadawa tarkon ‘yan ramuwar gayya ko batagari.
Sannan idan ya zamana dole ne sai kin yi amfani da kafofin sadarwa na zamani, to, ki kula da wadanda kike tattaunawa da su, kada ki sanya hotunanki ko ba da adireshinki ga duk mutumin da ba ki yarda da take-takensa ba. Domin a matsayinki na ‘ya mace, ya kamata a ce duk lokacin da kuke tattaunawa da mutum – kai-tsaye ko ta kafar sadarwa, to, ki tsaya ki lura da manufarsa a kanki.  
Abu na karshe, shi ne, dole ne sai al’ummar mu ta zama mai lura da kai-kawon mutanenta da bakin fuskar da suke shigowa. A nan za ka yi mamaki idan ka ga yadda muke zaman ‘yan marina a unguwanninmu, ta yadda makoci bai san halin da makocinsa yake ciki ba. Amma ina mamakin yadda za a shiga gidan matar aure a yi mata fyade, a kashe ta ba tare da mutanen unguwa sun ji kuma sun kawo dauki ba.
Daga karshe bayan mun yi wa wadannan mata da suka rasa ransu ta hanyar wannan ta’addanci addu’ar Allah ya jikansu da rahamarSa, dole ne mu yaba wa hukumar ‘yan sanda ta Jihar Kano, musamman mai girma Kwamishina watau Muhammad Musa Katsina bisa jajircewar da ya yi wajen sai an zakulo tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aiki a gaban kuliya.
 Mariya Tijjani Maibiskit
daliba ce a sashen koyar da aikin jarida na Kwaklejin Kimiyya da Fasaha ta Kano (Kono Polytechnic)
0809 470 7758

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno