Fyade: Kotu ta ba da umarnin a jefe wani tsoho a Kano

Wata kotun Shari’ar Musulunci da ke Nomansland a birnin Kano ta yanke hukuncin kisa ga wani tsoho mai kimanin shekara 63 ta hanyar jefewa da duwatsu sakamakon samunsa da laifin yi wa wata yarinya ’yar shekara 10 fyade da kuma harbinta da cutar kanjamau.A takardar karar da magatakardar kotun Uba Alasan Rimi ya gabatar ya […]

Fyade: Kotu ta ba da umarnin a jefe wani tsoho a Kano
Fyade: Kotu ta ba da umarnin a jefe wani tsoho a Kano

Wata kotun Shari’ar Musulunci da ke Nomansland a birnin Kano ta yanke hukuncin kisa ga wani tsoho mai kimanin shekara 63 ta hanyar jefewa da duwatsu sakamakon samunsa da laifin yi wa wata yarinya ’yar shekara 10 fyade da kuma harbinta da cutar kanjamau.
A takardar karar da magatakardar kotun Uba Alasan Rimi ya gabatar ya ce kimanin wata hudu da suka gabata tsohon mai suna Ubale Sa’idu Dotsa da ke da cutar kanjamau ya yi wa yarinyar wacce aka boye sunanta fyade lamarin da ya jawo ta kamu da cutar.
Mutumin da ake zargi ya amsa laifinsa, inda ya ce tsautsayi ne ya kai shi ga aikata wannan laifi. “Yarinyar ta dade tana zuwa wurina, amma ina korarta. Sai dai da yake komai mukaddari ne kuma tsautsayi ba ya wuce ranarsa har wata rana ta ribace ni na neme ta.”
Da aka tambayi tsohon ko ya san yana dauke da cutar kanjamau, ya tabbatar da hakan, sai dai ya nemi kotu ta yi masa sassauci cikin hukuncin da za ta yanke masa.
Alkalin kotun Mai shari’a Faruk Ahmad ya yanke wa tsohon hukuncin kisa ta hanyar jefewa da duwatsu, ganin cewa shi magidanci ne kuma ya aikata laifin ne bisa ganganci.
A karshe kotun ta nemi magatakardarta ya rubuta takarda ga ofishin Gwamnan Jihar Kano, domin jin ra’ayinsa game da hukuncin da ta yanke wa tsohon.