Fyade: Kotu ta tsare Mai Siket a gidan yari

Kotun Majistare da ke zamanta a Noman’s Land, Kano, ta tsare wani matashi a gidan yari bisa zargin yi wa mata 40 fyade. Matsahin wanda ake wa lakabi da Mai Siket, ya amsa a gaban kotun cewa ya yi fyade ga matan, cikinsu har da wata tsohuwa, a garin Kwanar Dangora, amma yana neman sassauci. […]

Fyade: Kotu ta tsare Mai Siket a gidan yari

Wadume: Kotu da dage sauraron shari’ar kisa

Kotun Majistare da ke zamanta a Noman’s Land, Kano, ta tsare wani matashi a gidan yari bisa zargin yi wa mata 40 fyade.

Matsahin wanda ake wa lakabi da Mai Siket, ya amsa a gaban kotun cewa ya yi fyade ga matan, cikinsu har da wata tsohuwa, a garin Kwanar Dangora, amma yana neman sassauci.

Mai Shari’a Muhammad Idris ya umarci a tsare Mai Siket a gidan yari a ci gaba da bincike, a kuma sama masa lauyan da zai kare shi

Mutanen Kwanar Dangora sun yi tururuwa domin shaida yadda shari’ar za ta gudana a kotun, wadda ta dage sauraren shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Yuli.

A cikin watan Yuni Aminiya ta kawo rahoton yadda ‘yan banga suka kama wani matashi tsirara da tsakar dare bayan an koro shi daga wani gida da ya yi kutse domin yin fyade a garin na Kwanar Dangora.

Bayan ya shaida musu cewa ya yi wa mata da kananan yara kimanin 40 fyade a cikin shekara guda a garin ne aka mika shi ga Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a kotu.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50