Fyade: Kuto Ta Tsare Magidanci A Gidan Yari A Zariya
Magidancin da kokarin yi wa yarin ]yar ’yar shekara bakwai fyade a unguwar Tudun Jukun
Kotun Musulunci da ke Tudun Wada Zariya ta tasa keyar wani magidanci dan shekara 52 bisa yunkurin yin fyade ga ’yar makwabcinsa.
Ana zargin magidancin da kokarin yi wa yarin yar ’yar shekara bakwai fyade ne a unguwar Tudun Jukun da ka Karamar Hukumar Zariya.
Bayan da aka karanta wanda ake zargin tuhumar da ake masa a karkashin sashi na 116 SPC ta Jihar Kaduna, alkalin kotun, Malam Mustapha Muhammed Abdullahi, ya tura shi gidan yari.
Daga nan kuma ya dage sauraron shari’ar zuwa Ranar 12 ga watan Satumba domin samu shawara daga ma’aikatar shari’a.