Fyade: Ya kamata gwamnati ta kafa kotunan musamman
Majalisar Tarayya ta bukaci Gwamnati ta kafa kotuna na musamman domin yanke hukunci da sauri ga masu aikata fyade da cin zarafi da ke karuwa a Najeriya. Da yake gabatar da kudurin, Unyime Udem ya ce fyade da cin zarafi sun karu a Najeriya a lokacin cutar coronavirus, sannan rahoton ‘yan sanda ya nuna an […]
Majalisar Tarayya ta bukaci Gwamnati ta kafa kotuna na musamman domin yanke hukunci da sauri ga masu aikata fyade da cin zarafi da ke karuwa a Najeriya.
Da yake gabatar da kudurin, Unyime Udem ya ce fyade da cin zarafi sun karu a Najeriya a lokacin cutar coronavirus, sannan rahoton ‘yan sanda ya nuna an yi fyade 717 daga watan Janairu zuwa Mayun bana.
“Haka na nufin an samu fyade 143 a kowane wata, wato kusan sau biyar a kullum, baya ga wadanda ba a samu rahotonsu ba”, inji dan majalisar, wanda ya ce saurin yanke hukunci zai kawo tsafta, domin hakan zai zama darasi ga masu niyyar aikatawa.
Majalisar ta umarci kwamitocinta na harkokin mata da ci gaban al’umma, ma’aikatar shari’ah ta gwmnatin tarayya da kungiyoyin kare hakkin bil’Adama su yi aiki tare da hukumomin da abun ya shafa sannan ya mika mata rahotonsa a cikin sati biyu.
Da yake jaddada muhimmancin magance matsalar da wuri domin tseratar da al’umma, dan majalisa Unyime Udem ya bukaci a yi tsauraran dokoki a kan matsalar wadda “keta hakki ne da tauye ‘yancin mutum na zabar yadda zai tafiyarsa da alakarsa da wani jinsi”.
Ya kuma yi kira ga Gwamnati da ta rika wayar da kan ‘yan kasa a kan fyade da cin zarafi ta hanyar yayata illolinsu, “domin kara fadakarwa a kan fyade da cin zarafi zai sa su gane cewa yaki da miyagun ayyukan nasu ne.
“Dole mu la’anci fyade da dangogin cin zarafin mata, mu dage da yakar su, mu kuma tabbatar cewa masu aikatawa sun fuskanci hukunci mai tsanani daga hukumomin da abun ya shafa”.
Dan majalisar ya ce, akwai bukatar yanke hukunci da sauri a kan “fyade da sauran laifuffuka masu alaka da shi” a Kotuna.
“Al’umma a fusace suke game da fyade da dangoginsa da ake wa mata da yara kanana (Mata) wadanda a wani lokaci ta kan kai ga rasa rayukansu.
Abun na da matukar ban tsoro a wannan lokaci duba da yadda laifuffukan suka yadu a tsakanin al’umma”.
Sai dai ya ce, ya kamata a rika ba wa wadanda aka yi a wa fyade kulawa da kwarin gwiwa su rika fitowa suna fadin abun da ya same su.”