Fyade: Yadda aka yaudari diyata da shinkafa da kwai
Mahaifin wata yarinya mai shekara shida da aka yi wa fyade, Okehelem Palace Oyenma, ya kirayi Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da ta tabbatar an bi wa diyarsa hakkinta. Lamarin ya faru ne a ranar 4 ga watan Yuli, inda wani matashi, ya zakkewa karamar yarinyar a unguwar Uwelu daura da titin Edobor a Karamar Hukumar […]
Mahaifin wata yarinya mai shekara shida da aka yi wa fyade, Okehelem Palace Oyenma, ya kirayi Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da ta tabbatar an bi wa diyarsa hakkinta.
Lamarin ya faru ne a ranar 4 ga watan Yuli, inda wani matashi, ya zakkewa karamar yarinyar a unguwar Uwelu daura da titin Edobor a Karamar Hukumar Egor ta Jihar Edo.
- Ambaliya ta kashe magidanci da iyalansa a Kebbi
- Yadda aka yi wa karamar yarinya yankar rago a Filato
Da yake zantawa da manema labarai, yayin wata zanga-zanga da aka gudanar a ofishin kungiyar ’yan jarida ta Najeriya reshen Jihar Edo, Oyenma ya yi zargin cewa matashin ya yaudari ’yarsa ne da shinkafa da kwai gabanin ya keta mata haddi.
Ya ce ya gano an ci zarafin diyar tasa ne yayin da jini ya rika fita daga farjinta babu kakkautawa.
Ya ce, “Ya daukar min diya ya kai ta bayan gidansa, inda ya bata shinkafa da kwai.
“Diyar tawa ta fada min cewa bayan ya ba ta abinci ta ci ta koshi, sai ya kwale mata kamfan da ke jikinta”, kuma ya fara sa mata yatsunsa sannan gabansa cikin al’aurarta.
“A daren da abin ya faru, mun rika neman diyar tawa da ni da ’yan sintiri amma muka rasa ba tare da sanin tana tare da Obiyan a gidansa ba.
- Ambaliya ta kashe magidanci da iyalansa a Kebbi
- Yadda aka yi wa karamar yarinya yankar rago a Filato
“Bayan mun gano ta kuma muka ga jini na tsiyaya daga jikinta. Mun nemi ta kai mu gidan wanda ya yi mata wannan aika-aika amma ta ce ba za ta iya gane gidan cikin duhun dare ba.
“Saboda haka washegari ta kai mahaifiyarta har gidan yayin da ni kuma na tafi debo ’yan sanda.”
“A yayin da muka isa gidan tare da jami’an ‘yan sanda, mun riski Obiyan tare da wani malamin tsubbu.
“A cikin farfajiyar gidan akwai wani kyalle duk jikinsa jini da kuma wasu layu da aka jera a tsakar dakin saukar baki.
“Daga nan kawai sai jami’an ’yan sandan suka ci kugunsa tare da malamin tsubbun”, inji mahaifin yarinyar.
Yayin da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, SP Chidi Nwanbuzor, ya tabbatar da faruwar wannan lamari da cewa da zarar an kammala bincike za a gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu.