G-Fresh da Babiana sun nemi a saki Baɗejo
Sojoji sun kama Badejo ne a watan Disamban 2024, biyo bayan wata taƙaddama tsakanin wani Janar ɗin soja da makiyaya.
Taurarin Tiktok biyu, G-Fresh da Hafsat Babiana, sun roƙi Gwamnatin Tarayya da rundunar sojin ƙasa, da su taimaka wajen sakin Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Baɗejo.
A ranar 9 ga watan Disamban 2024 ne, sojoji suka kama Baɗejo a ofishinsa da ke Jihar Nasarawa.
- DAGA LARABA: Yadda sunayen zamani suka shafe na Hausawa
- NFF ta naɗa Éric Chelle a matsayin sabon kocin Super Eagles
An kama shi ne saboda wata taƙaddama da ta faru tsakanin wasu makiyaya da wani tsohon Janar ɗin soja a unguwar Tudun Wada da ke Nasarawa.
Iyalan Baɗejo sun bayyana cewa rikicin ya faru ne bayan tsohon Janar ɗin ya buɗe wa shanunsu wuta.
A cewarsu hakan ne ya sanya makiyayan kare kansu, tare da ƙwace bindigar Janar ɗin, sannan suka kai wa ‘yan sanda rahoto da kuma Baɗejo a matsayin shugabansu.
Kwanaki kaɗan bayan faruwar lamarin, sojoji suka kama Baɗejo.
Sai dai, G-Fresh da Babiana sun bayyana cewa suna roƙon shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Christopher Musa, da shugaban NSA, Nuhu Ribadu, da su taimaka a saki Baɗejo.
A cikin bidiyon da suka fitar, sun bayyana Baɗejo a matsayin mutumin kirki, inda suka roƙi gwamnati da ta shiga lamarin don ganin an sake shi.