G5: Wike da sauran Gwamnonin da suka yi wa PDP zagon kasa na ganawa da Tinubu

Ana ganin sun taimaka wa nasarar Tinubu

G5: Wike da sauran Gwamnonin da suka yi wa PDP zagon kasa na ganawa da Tinubu

Gwamnonin G-5

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, yanzu haka yana ganawa a Fadar Shagaban Kasa da mambobin rusasshiyar kungiyar G-5 ta Gwamnonin da suka yi wa jam’iyyar PDP zagon kasa a zaben da ya gabata.

Kungiyar dai ta kunshi Gwamnoni biyar, wadanda dukkansu ’yan PDP ne, amma suka yi adawa da takarar Atiku Abubakar da jagorancin dakataccen shugabanta, Iyorchia Ayu.

Gwamnonin sun hada da Seyi Makinde na Oyo da tsofaffin Gwamonin Ribas (Nyesom Wike) da na Abiya (Okezie Ikpeazu) da na Enugu (Ifeanyi Ugwuwanyi) da kuma Binuwai, Samuel Ortom.

Ana hasashen rawar da suka taka wajen yi wa PDP zagon kasa ta taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Bola Tinubu na APC a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Idan za a iya tunawa, daga makon da ya gabata zuwa yanzu, tun bayan rantsar da Tinubu, Wike da Makinde sun yi ta ziyartar Fadar Shugaban Kasa ba kakkautawa, a daidai lokacin da ake shirin kaddamar da Majalisar Dokoki ta 10.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta