…Ga alama Tinubu bai ji dadi ba

Jim kadan da bayyana sunan Farfesa Yemi Osinbanjo a matsayin wanda zai mara wa Janar Buhari baya a takarar shugabancin kasa, jigo a jam’iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sanarwa ga manema labarai, inda ya bayyana dalilansa da suka sanya ya janye daga neman wannan mukami na Mataimakin Shugaban kasa a jam’iyyar […]

…Ga alama Tinubu bai ji dadi ba

Jim kadan da bayyana sunan Farfesa Yemi Osinbanjo a matsayin wanda zai mara wa Janar Buhari baya a takarar shugabancin kasa, jigo a jam’iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya fitar da sanarwa ga manema labarai, inda ya bayyana dalilansa da suka sanya ya janye daga neman wannan mukami na Mataimakin Shugaban kasa a jam’iyyar tasu, inda daga dukkan alamu ta tabbata cewa bai ji dadin zabin da aka yi ba.
“Na yi aiki tukuru domin ganin jam’iyyar nan ta bunkasa, ta yadda za ta iya cin kowane irin zabe kuma ta ba da shugabancin da kasar nan ke bukata. Babu abin da ya fi muhimmanci kamar ganin mun samu wannan biyan bukata, ba don ni ba sai domin al’umma da kuma kasata da nake kauna.” Inji Tinubu, a takardar tasa.
Tinubu ya ci gaba da bayyana irin yadda ya yi ta fadi tashi domin ganin cewa an samu tabbatar da jam’iyyar, sannan ya nuna cewa Janar Buhari tun da farko ya yi masa tayin zama Mataimakin Shugaban kasa, tayin da ya ce ya amsa, amma ya ce wasu ’yan bakin ciki suka sako al’amarin addini suka lalata wannan buri nasa. Sai dai duk da haka, ya ce ya hakura da mukamin, ba don komai ba sai domin a samu nasara.
Kamar yadda ya ce: “Wannan lokaci ne na bukatar hada hannu domin cin ma burin da ke gabanmu. Lallai ne mu yi kokarin murkushe abokan gabar mu kuma mu kaurace wa duk wani kwadayi, domin kauce wa yakar junanmu da ake son ganin mun yi.”
Daga karshe kuma Tinubu, wanda shi ne tsohon Gwamnan Jihar Legas, ya karkare jawabinsa da cewa: “Na sadaukar da kaina da gaske domin ganin cewa mun cin ma kudurin Janar Buhari da Farfesa Osinbajo, na ganin an ceto Najeriya daga balbalcewa.”
Ganin yadda jigon jam’iyyar ya fitar da wannan takarda cikin sauri da kuma irin maganganun da ya rika fitarwa cikin boyayyun kalmomi, wasu na ganin cewa lallai bai ji dadin hana shi mukamin Mataimakin Shugaban kasa da aka yi ba. Wasu ma na ganin cewa akwai yiwuwar ya dauki wani boyayyen mataki da ba zai wa jam’iyyar dadi ba nan gaba.