Ga barawo ga mai kaya
Wani mai tura baro ne sai wani barawo ya sato buhun wake ya ba shi dako, to da barawon ya ga cewa mai kaya ya gano shi, sai ya gudu ya bar dan baro da buhun wake aka kama shi, ya ce shi fa dako aka ba shi. Ina wanda ya ba shi dako? Babu […]
Wani mai tura baro ne sai wani barawo ya sato buhun wake ya ba shi dako, to da barawon ya ga cewa mai kaya ya gano shi, sai ya gudu ya bar dan baro da buhun wake aka kama shi, ya ce shi fa dako aka ba shi. Ina wanda ya ba shi dako? Babu shi babu alamarsa, ya gudu. Da aka je caji ofis, na fara yi masa tambayoyi, sai ya ce: “Dandan dandan dandan! Ga barawo, ga mai kaya.” Sannan sai ya dubi dan sandan da ke yi masa tambayoyi ya ce: “Yallabai me kake jira ga ka da bindiga ka harbe ni kawai.”
Daga Salihu Makera, 07086866165.