Ga Gwamna Babagana Zulum

Muna taya Mai girma sabon Gwamnan Jihar Borno murnar kama aiki. Allah Ya taya shi riko Ya sa ya gama lafiya. Bayan haka muna rokon Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi wa Allah ya taimaka wajen tsara yadda al’ummar Karamar Hukumar Abadan za su koma gidajensu a garuruwan da Boko Haram suka kore su […]

Ga Gwamna Babagana Zulum
Ga Gwamna Babagana Zulum

Muna taya Mai girma sabon Gwamnan Jihar Borno murnar kama aiki. Allah Ya taya shi riko Ya sa ya gama lafiya. Bayan haka muna rokon Gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi wa Allah ya taimaka wajen tsara yadda al’ummar Karamar Hukumar Abadan za su koma gidajensu a garuruwan da Boko Haram suka kore su a baya.

Hakika mutanen yankin suna cikin kunci, saboda babu yadda za a yi mutum ya shafe shekara shida yana zaman gudun hijira a ce rayuwarsa tana tafiya daidai. Muna fata a samar da tsaro a yankin a mayar da jama’a gidajensu. Kuma muna rokon a nada mana Shugaban Karamar Hukuma ma kishi da son jama’a kafin Gwamna ya gudanar da zaben kananan hukumomi da ya yi alkawari a nan gaba.  Mu kuma jama’ar yankin ya kamata mu rika taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro.

Daga Rawagana Abubakar, Mai sayar da huluna Mpape, Abuja 08066250645.

 

Fatan alheri ga Gwamna Masari

Assalam. Edita ka ba ni fili in mika godiyata ga Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari a kan irin kokarin da yake na raya jihar  da al’ummar jihar. Muna godiya kan irin ayyukan alheri da Mai girma Gwamna Masari yake yi a Jihar Katsina da fatan Allah Ubangiji Ya kara ba shi damar ci gaba da ayyukan alherin da yake yi amin.

Daga Sagir Saminu Kaita, Masoyin Jaridar Aminiya, 08133522467.

 

Kira ga sarakunanmu na Arewa

Salam Aminiya. Ina kira ga sarakunanmu na Arewa ku yi koyi da Basaraken nan na Kagara, Danmajan Kagara wanda ya bai wa Fulani gudunmawar Naira miliyan 3 da buhun dawa 10 akan wata shari’a da wani alkali ya yi na rashin iya shari’a. Allah Ya sa sarakunan Arewa su ci gaba da irin wannan taimako.

Daga Adamu Sulaiman Kaugama, Sauna Kano 08088227962.

 

Sabuwar majalisa, sabon tsari

Assalamu alaikum Edita. Ina taya Majalisar Dokoki ta Kasa karo na 9 murnar fara aiki. Allah Ka bai wa sababbin shugabannin majalisun damar aiwatar mana da aiki yadda ya kamata da kuma kawo mana ci gaba mai amfani a daukacin kasar nan. Daga karshe ina kira ga ’yan Majalisar Wakilai da ta Dattawa su kawar da bambance-bambacen jam’iyya ko yanki su hada kai domin ciyar da Najeriya gaba.

Daga Alhaji Abbas Baffah, Cheledi Jihar Bauchi. 08072052816.

 

Fatan alheri  ga Sanata Lawan 

Assalamu  alaikum  Edita. Mu al’ummar  Arewa maso  Gabashin  Najeriya muna  bayan  Sanata Ahmed  Lawan dari  bisa  dari wanda  ya zama Shugaban  Majalisar  Dattawa saboda  jajircewa da yake yi  na ganin an ciyar da wannan kasa gaba. Muna  addu’ar  Allah Ya ba shi nasara, amin.

Daga Garba  Sabiyola  Sa’idawa,  Gashuwa 07061636664.

 

Shawara ga Buhari kan masu garkuwa da mutane

Assalam Edita. Don Allah ina son ka ba ni dama domin in bai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawara a kan wannan masifa da ke damun Arewacin kasar nan ta yadda ’yan ta’adda ke yin garkuwa da jama’a don neman kudin fansa. Shawarata ita ce, tunda mutanen nan ana ganinsu ba aljannu ba ne ya kamata gwamnati ta ta kirawo su a yi zama da su domin a yi sulhu. Durkusa wa wada ba gajiyawa ba ne. Shawara ta karshe gwamnati ta fitar da kudi ta bai wa malaman addinin Musulunci da na Kirista a kama yin addu’a a kan Allah Ya sauwake mana wannan masifa.

Daga Hadi Tsohon Sarki, Daura. 07015256836.

 

Farfado da ilimi: Kira ga

Gwamna El-rufai

Salam Edita. Bayan gaisuwa ina yaba wa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i a bisa kokarinsa na farfado da ilimi a jihar, musamman bangaren firamare, inda ya wadata wasu wurare da sababbin ajujuwa, da samar da littattafan koyarwa na zamani da kayan koyo da koyarwa ga malaman jiha da samar da daukar sababbin darussa don samun ingantacce kuma nagartaccen ilimi. Mun ji kuma mun gani dole ne mu yaba maka. Sai dai duk da wadannan abubuwa da ka tanadar ga ilimi a wannan jiha malaman jiharka musamman na firamare suna matukar cikin kuncin rayuwa, inda ba a kulawa da walwala da jin dadinsu, albashinsu ba a biya a kan lokaci, abin takaici ma ba a la’akari da yanayi. Don Allah a rika sara ana duban bakin gatari.

Daga Basiru Danbazazzagi, 08058591624.

 

Kirkiro da masaratu: Jinjina ga Gwamnatin Kano

Assalam. Fatan alheri a gare ku AMINIYA. Don Allah Edita a taimake ni a ba ni dama, in yi jinjina ga Gwamnatin Kano da ’yan majalisarmu ta jihar Kano bisa kirkiro masarautu hudu da ta yi, tare da mika musu sanda. Wannan al’amari ya burge ni domin tuntuni ya dace a ce an yi hakan, amma babu komai jinkirin ma alheri ne. Ina kuma taya masu martaba sababbin sarakunan murna tare da addu’ar Allah Ya yi riko da hannunsu, domin sauke nauyin da aka dora musu. Da fatan dagatai da hakimai da limamai za a yi mubaya’a ga sababbin sarakunan.

Daga Murtala Ahmed Abubakar, Kwalli Gidan Doki, Kano, 07068295953.

 

Kira ga Gwamnatin Jihar Kano

Don Allah muna so Gwamnatin Jihar Kano ta gyara mana hanyar Riruwai, kuma ba mu da wutar lantarki ba mu da ruwa ba mu da kayan more rayuwa. Mai girma Gwamna da kanka ka gani da ka je, muna cikin matsala. Allah Ya ba ka tsawon kwana, insha Allahu sai ka kai Shugaban Kasa. Allah Ya yi maka jagora kuma ’yan jarida Allah Ya kara yi muku daukaka.

Daga Zulaihat Musa Bala Riruwai, 08143418713.

 

Ga Kanawan Dabo

Edita ba ni fili don girman Allah in kara tunatar da Kanawa cewa, Allah ke da zamani kuma Shi Ya kawo zamanin da Gwamnatin Jihar Kano ta daddatsa kasar Kano zuwa masarautu 5 masu cin gashin kansu. Babu abin da ya rage mana yanzu sai godiyar Allah da addu’a da fatan Allah Ya sa hakan ya zama alheri.

Daga Amiru Isah Bakori, 07068147933.    

 

Kira ga Gwamnatin Kebbi

Salam Edita. Ka ba ni dama in yi kira ga Gwamnati Jihar Kebbi mai albarka ta maido da ba da magani ga marasa lafiya da suka shafi kwakwalwa domin wallahi hakan ya taimaka wa mata sosai amma a yanzu da ba sa samun magani matsalolin na son dawowa. Allah Ya albarkaci Jihar Kebbi.

Daga Mansir Dan Alhaji, 07032289946

 

Shaye-shayen matasa a Katsina

Salam, yaya aiki. Don Allah ku mika mini kirana ga mahukuntan Jihar Katsina su taimaka mana wajen dakile karuwar shaye-shaye da suka addabi matasanmu. Ina fatan Allah Ya ba da ikon daukar mataki.

Daga Aliyu Ibrahim, 09078477886.

 

Kira ga Shugaba Buhari

Assalam. Ina kira ga Shugaba Buhari game da yawan hadarin da ake samu a kasar nan. Kamata ya yi a sa doka mai tsanani a kan duk wanda aka kama da laifin haddasa hadari lokacin obatakin. Ba komai ke kawo hadari ba face obatakin da fatan kuma dokar ba za ta tsaya a iya talaka ba za ta hau kan kowa daga kan ma’aikata da ’yan sanda da masu kudi har zuwa kan masu mukamai don wadannan su suke fara karya doka a kasar nan. Kuma in abu ya faru aka kama su a wajen sai su nuna su wadansu ne kuma a wajen za a rabu da su. Wannan ba adalci ba ne kamata ya yi in an sa doka ta hau kan kowa, ba iya talaka ba.

Daga Nasir Birged, Kano 09069985179.

 

Ganduje ba karin masarautu

muke so ba

Asslam Edita, ina fatan kana lafya. Don Allah ka ba ni fili domin in shaida wa Gwamna Ganduje cewa, Kano ba karin masarautu muke so ba, abubuwan more rayuwa muke bukata. Kun ce ba kudi, kun ki biyan ma’aikata kudin sallama daga aiki, yanzu a ina za ku samo kudin tafiyar da wadannan masarautu?

Daga Husaini Tsoho Imawa Kura, 08027911150.

 

Kira ga shugabannin Dambatta

Assalam Edita. Zuwa ga shugabanninmu na Karamar Hukumar Dambatta, me ya sa aka ki gyara mana wutar lantarkinmu kusan shekara 10, inda garuruwa kusan 6 suke amfana da ita ko mu ba mu da hakki a gwamnati ce?

 Daga Yusuf Liman Sansan, 09038561848.

 

Ta’aziyya ga iyalan  Sharif Rabi’u Usman

Salamu alaikum Edita. Ina son a taimaka min don girman Allah in mika gaisuwar ta’aziyya ga iyalan Sharif Rabi’u Usman Baba. Allah Ya yi masa rahama don girman ManzonSa (SAW).

Daga Gambo Aminu, Barnawa Kaduna 08021454493.

 

Martani ga Adam A Zango

Zuwa ga Adamu A Zango, wai ka ce kai ne Bahaushen da ya fi kowa (suna) a duniya. Ni kam na ce tun a suturar da ke jikinka ta karyataka. Ka dubi wuyanka har da sarka ga wata hula da mu Hausawa muke kiranta hana Sallah a kanka, ko a nan ka fadi warwas. Kai idan ma tsantsar Hausa ce ba sai an je da nisa ba, wallahi ba za ka hada kanka da Aminu Alan Waka ba.

Daga Angon Raheenat K. M., Kano 08063844790.

 

Hukuncin kotu kan Jihar Zamfara

Assalam jaridar Aminiya. Babban Jojin Najeriya muna godiya kan hukuncin da ka yanke kan zaben Jihar Zamfara. Gaisuwa ga Editan Aminiya.

Daga Zayyanu Usman Kokiya, Birnin Magaji, 08146892660.

 

Kira ga Gwamnan Katsina

Edita ka ba ni dama in mika kira ga Gwamnan Jihar Katsina kan ya taimaka a kawo mana da jami’an Hukumar NDLEA a sassan jihar domin dakile shaye-shayen da suka addabi matasanmu.

Daga Ibrahim KSD, 08031944943.