Ga masu son Buhari ya zama ‘kun fa yakunu’

Abu ne sananne ga kowane dan Najeriya cewa al’amura sun jagwalgwale a kasar nan, kuma sakamakon wannan jagwalgwalo ne ya sanya al’ummar kasar nan suka tashi tsaye a zaben da ya gabata suka tabbatar sun kawar da gwamnatin Jam’iyyar PDP wadda ta shafe shekara 16 tana mulkin kasar  nan.’Yan Najeriya sun tumbuke mulkin PDP wadda […]

Ga masu son Buhari ya zama ‘kun fa yakunu’
Ga masu son Buhari ya zama ‘kun fa yakunu’

Abu ne sananne ga kowane dan Najeriya cewa al’amura sun jagwalgwale a kasar nan, kuma sakamakon wannan jagwalgwalo ne ya sanya al’ummar kasar nan suka tashi tsaye a zaben da ya gabata suka tabbatar sun kawar da gwamnatin Jam’iyyar PDP wadda ta shafe shekara 16 tana mulkin kasar  nan.
’Yan Najeriya sun tumbuke mulkin PDP wadda ta sha alwashin mulkar kasar nan zuwa shekara 60 ne, sakamakon yadda ta gaza sarrafa dimbin dukiyar da Allah Ya ba kasar nan a daidai lokacin da ta zo gadon mulki da kuma uwa uba yadda tattalin arzikin kasar ya rika tabarbarewa sakamakon mahaukaciyar sata da almundahanar da shugabanni da ’yan siyasa suka rika tafkawa. To, amma ba wannan ne babban abin da ya fi daga hankalin ’yan Najeriya domin sun saba da wannan mugun hali na shugabanni na nuna halin bera, babban abin da ya fi daga musu hankali shi ne yadda kiri-kiri kasar ta koma tamkar kwata ko’ina sai zubar da jini da zaman fargaba.
Tashin bama-bama wanda ya faro daga ranar 1 ga Oktoban shekarar 2010 a Dandalin Eagle Skuare da ke Abuja, kafin majanuniyar kungiyar na ta Boko Haram ta dauki wannan salo, ya zama kusan kullum. Dubban jama’a sun rasa rayukansu sakamakon ayyukan ’yan ta’addar Boko Haram, in ma ta hanyar tashin bama-bamai ko ta hanyar bindige su a gidaje ko a wuraren ibada ko a kasuwanni ko a makarantu ko tashoshin mota ko a bankuna kai hatta a asibiti ma ba a tsira ba. A Kudu kuma ga bala’in satar mutane ana garkuwa da su ana neman miliyoyin Naira daga iyalai ko dangin wadanda aka kama wani lokacin ma a kashe wanda aka kama. Sannan ga matsalar matsafa da gidajen kyankyasar jarirai inda ake killace ’yan mata a rika kai karti suna lalata da su, idan suka haihu a sallame su da ’yan kudin kadan jariran kuwa a sayar ko a yi tsafi da su da sauran miyagun ayyuka da kai ka ce dujal ya bayyana.
A tunanina ko dan tayin da yake cikin mahaifiyarsa ya ji a jikinsa cewa kasar nan tana cikin mummunar hali, kasar nan tana bukatar mai ceto kasar nan tana bukatar wani mai sadaukarwa don ceto ta daga wannan hali na ha’ula’i.
Muna cikin wannan hali da ya wuce ‘min sharrin’ Allah cikin ikonSa da rahamarSa Ya jikanmu aka samu juyin juya-hali a ruwan sanyi aka kawar da gwamnatin da duniya ma ta yarda ta gaza hatta a cikin magoya bayan Jam’iyyar PDP mai mulkin kasar a lokacin akwai wadanda suka yarda ta gaza, aka zabi Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban kasa. Muhammadu Buhari ya zo ne a daidai lokacin da kusan komai ke neman tsayawa a kasar nan. Babu zaman lafiya.. babu man fetur… babu wutar lantarki… babu albashi… babu…babu ga su nan dai barkatai.
Hatta kasashen Turai da Amurka da ake ganin kaskoki ne da suke rabar kasashe irin Najeriya mai arzikin man fetur, sai da suka dawo suna tausaya mana ganin cewa komai na neman tsayawa cik ciki har da numfashinmu. Sun shaida wa duniya cewa lallai su ma sun yarda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya iske Najeriya a mawuyacin hali, kuma yana bukatar tallafi da taimako don fitar da Najeriya daga mummunan halin da take ciki.
Sai dai babban abin takaici, ko kwana 30 Shugaba Muhammadu Buhari bai yi a gadon mulki ba, mutane suka fara guna-guni wai yana tafiyar hawainiya. Mutane suka fara kukan suna so su ga canjin da ya yi alkawari su fa har yanzu jiya i yau.
Ga masu irin wannan tunani so suke Buhari ya zama wani ‘kun fa yakunu,’ wato ya ce wa abu kasance sai ya kasance. Sun manta cewa shekara da shekaru aka dauka ana rusa kasar nan ana tafka barna da talababbiya. Sun manta cewa gyara ya fi barna wuya ko kuma sun sani amma da gangan suke irin wadannan maganganu.
Kowa yana jin irin mahaukaciyar satar da aka tafka musamman a shekara shida da suka gabata, wadda aka ce hatta shi kansa tsohon Shugaban kasa Jonathan yana mamakinta. Sannan mu dauki bangare daya kawai wanda ya fi komai muhimmanci wato tsaro, don Allah wa ya taba tunanin cewa ’yan Boko Haram sun daddasa bama-bamai a kan hanyoyin wasu garuruwa na jihohin Arewa maso Gabas? Amma yau ga shi an gano haka ana ta kokarin ciccire su domin a samu kaiwa ga garuruwa da kauyukan da suka kame suke garkuwa da mutane. Ana ci gaba da kwato garuruwa tare da gano wasu hanyoyi da suke samun makamai da kayan aiki ana dodewa. Ana ceto dimbin mutanen da suka yi garkuwa da su, ana dakile yunkurin wasu hare-harensu har ta kai ana yi musu kamun kazar kuku. A baya idan aka ce ga ’yan Boko Haram nan suna zuwa ba fararen hula ba, hatta sojoji gudu suke yi, amma yau ‘’yan banga ma tsayawa suke yi su fafata da su.
A bangaren almundahana da satar kudin jama’a muna ta jin bayanan yadda aka yi watandar kudin kasar nan, kuma ana ta samun ci gaba wajen samun bayanan inda aka kai kudaden da wadanda suka karkatar da su, da yadda ake satar man kasar nan da masu satar.
Galibin jihohin da suka kasa biyan albashi wata da watannin suna ta kokarin warware bashin albashin da ake bin su, wasu ma sun biya sun huta. Amma abin takaici sai ka ji mutum ya tare ka a hanya yana cewa mu fa har yanzu ba mu ga canjin nan da ake fada ba. Tunaninsa canjin yana nufin ya ga tuwo da mai da nama a kwanon abincinsa ba tare da ya motsa ba… tunaninsa duk abin da ya taba ya zama Naira ko Dala… tunaninsa ya kwanta ya shantake amma ya rika wanke goma yana tsoma biyar… tunaninsa Buhari  ya mayar da Najeriya aljannar duniya nan take shi kuma ya yi ta shan lagwada a maho!
Ni dai ban zaci haka daga Buhari ba, bilhasali ma lokacin da zan jefa kuri’ata cewa na yi a zuciyata idan zan zabi Buhari ne don ni na ji dadi ’ya’ya da jikokina su ci gaba da shan wuya a gaba, kada Allah Ya ba Buhari nasara a zaben nan, amma idan zan zabi Buhari ne da niyyar in sha wuya amma ’ya’yana da jikokina su samu sa’ida a gaba, Allah Ya ba shi nasara. Shi ya sa lokacin da aka ce ya ci zabe ban taya shi murna ba, tausaya masa na yi har na ce bai sa’ar zuwa gadon mulki, domin sai kasar ta lalace ake nemansa, amma lokacin da take cikin yalwa ba a bukatarsa, ba a son irinsa a kusa da gadon mulki.
Don haka mu daina tunanin Buhari zai gyara komai da komai a kasar nan, mu dauka tare za mu hada hannu da shi mu yi wannan gyara, mu dauka zai dora dan ba ne na gyara sannan ni da kai da ke da shi da ita da mu da su, mu tashi tsaye wajen sadaukar da gyara don wannan gyara ya cimma nasara. Duk wanda yake tsammanin gyara Najeriya na Buhari shi kadai ne kuma mulkinsa lokaci ne na kwasar gara da daula to ku dauke shi daidai da mutumin da ke hango kawalweniya a kwalta kuma ya yi tsammanin ruwa ne. Don haka mutane su gane Buhari bai da ‘kun fa yakunun’ da zai gyara kasar nan kamar kiftawar ido.